An gano hanyoyi 2000 da ake fasa kwabrin shinkafa ta Arewacin Najeriya - Kwastam

An gano hanyoyi 2000 da ake fasa kwabrin shinkafa ta Arewacin Najeriya - Kwastam

Kwantrolan hukumar kwastam shiyar Zone B, jihar Kaduna, Mustapha Sarkin Kebbi, ya bayyana cewa hukumar ta gano hanyoyi 2000 da ake amfani da shi wajen fasa kwabrin shinkafa da wasu haramtattun kayayyaki ta Arewacin Najeriya.

Ya ce hukumar kwastam ba tada karfin ma'aikatan da zasu tsare dukkan wadannan barayin hanyoyin amma suna iyakan kokarinsu wahen tabbatar da cewa shinkafar wajen ba su shigowa Najeriya.

Kwantrolan wanda yayi hira da manema labarai ya zayyana wasu nasarori da yankinsa ta samu wajen dakile masu fasa kwabri.

DUBA NAN Yari mai ilimin addini ne kuma mai tsoron Allah - APC ta mayarwa Matawalle martani

Ya bayyana cewa an damke kayyaki da dama wanda ya hada da motoci, shinkafa, man gyada, taliya da sauransu a jihohin Katsina, Sokoto, Kebbi da Kwara . Kalli jerin abubuwan ya ce sun damke:

Motoci 25

Buhun shinkafa 703

Galolin man gyada 530

kwalayen taliya 245

dilan kayan gwanjo 9

Galolin Kalanzir 40

Tankar man fetur

Galolin man fetur 288

A bangare guda, Ministan sadarwa, Isa Pantami, ya shawarci hukumar kwastam ta kasa da ta dage dokar hana kai man fetur garuruwan da ke kusa iyakokin kasar nan. Hakan ya zama babban kalubalen da ma'aikatarsa ke fuskanta.

Kamar yadda takardar da ta samu jaridar Premium Times a ranar Juma’a, wacce mai magana da yawun minstan, Uwa Suleiman ta fitar, ta ce hakan zai bayar da dama kamfanonin sadarwa su tayar da injinan wutansu don samar da ayyukansu ga ‘yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel