Rusau: KASUPDA ta rushe gidaje 300 a Kaduna

Rusau: KASUPDA ta rushe gidaje 300 a Kaduna

Hankulan mazauna birnin Kaduna sun tashi, sakamakon rushe sama da gidaje 300 da cibiyar habaka birane ta jihar Kaduna (KASUPDA) ta yi. Wasu gidajen da aka rushe din ana kan ginasu ne, wasu daga ciki kuma an kammala har an tare.

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Lahadi, Yusuf Zomo, mai gidan haya a yankin, yayi magana a madadin wadanda abun ya shafa. Yace jami’an KASUPDA din sun iso yankin ne a ranar Juma’a, wajen karfe 12 na dare inda suka dinga rushe gidajen.

An gano cewa, da yawa daga cikin gidajen an rushe wani sassa ne nasu inda wasu kuma katanga kadai aka sauke musu.

Zomo ya ce jami’an KASUPDA din, wadanda suka samu rakiyar jami’an tsaro rike da bindigogi, sun iso yankunan ne da motocin ture gini.

Kamar yadda Zomo ya sanar, wuraren da abun ya shafa sun hada da: Babban Saura, Anguwan Waziri, Karji, Tsohon Kamanz da Anguwan Maigyero duk a kan titin Yakowa, Kaduna.

Da farko sun ce basu son ganin kwantena a kan titi kuma sun bukaci masu su da su kwashesu daga tituna. Mamallakansu sun bi umarni ta hanyar kwashewa,” in ji shi.

Da tsakar daren ranar juma’a, lokacin da mutane ke bacci suka iso inda suka fara rusau. Jami’an tsaro rike da bindigogi ne suka rakosu. Sun yi barazanar harbin duk wanda ya je kusa dasu. Mutane na barci aka dinga rushe gidajensu. Duk wanda bai fita ba a kanshi zasu rushe. Haka jama’a suka dinga gudu cikin tashin hankula,

“Idan gwamnatin nan na ikirarin filin nasu ne, me yasa basu zo da rana tsaka ba tare da sanar damu niyyarsu? Har yanzu bamu san dalilin rushe mana gidajenmu ba. Gwamna El-Rufai kuwa ya sani? Ba yakarsu zamuyi ba, amma mu muka zabesa.” Cewar Zomo,

A yayin maida martani, Ismaila Dikko, manajan daraktan KASUPDA, yace an yi gine-ginen ne ba bisa ka’ida ba. Ya ce, duk da jerin jan kunnen da aka yi wa jama’ar yankin, sun ki daina gine-ginen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel