Adegbite: Shugaba Buhari ya ba mu umarni a kan aikin Ajaokuta

Adegbite: Shugaba Buhari ya ba mu umarni a kan aikin Ajaokuta

Ministan arzikin kasa da ma’adanan Najeriya, Olamilekan Adegbite, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba su sabon umarni da cewa su karkare aikin kamfanin Ajaokuta.

Mai girma Olamilekan Adegbite ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taron shirya karawa juna sani da aka shirya a babban birnin tarayya Abuja. Za a yi wannan taro ne a Watan Disamba.

Ministan gwamnatin tarayyar ya yi jawabi ne ta bakin Hadiminsa na musamman, Sunny Ekozin. A cewar Ekozin, Ministan ya na bakin kokarinsa domin ganin ya cika umarnin shugaban kasar.

“A watanni ukun bayan nan, mu na ta kokari bakin gwargwado domin ganin mun samu cigaba a aikin kuma mu na farin cikin sanar da Najeriya cewa mu na da goyon bayan shugaban kasa.”

KU KARANTA: Adoke: Tsohon Ministan PDP ya nemi Interpol ta sake shi

“Cikakken goyon bayan da shugaban kasa ya ba mu ya kunshi mara mana baya ta fuskar siyasa domin ganin an karkare aikin Ajaokuta, kuma da ikon Ubangiji za a gama aikin kwanan nan.

Ministan ya ce wannan ya na cikin umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada domin shawo kan matsalolin da su ka dabaibaye harkar ma’adanai domin fadada tattalin arziki.

Adegbite ya ke bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kawo wani sabon tsari na hako ma’adanan cikin kasa. A cewar Ministan, ba a taba ganin irin wannan tsari a kasar ba.

“Haka zalika akwai kokarin inganta hako ma’adanan da ke cikin kasa a babban birnin tarayya Abuja da sauran jihohi 36 na Najeriya.” Wadannan ayyuka za su samar da aikin yi Inji Ministan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel