Da karfin bindiga aka ci zaben Jihar Kogi - Inji Lawrence Emehel

Da karfin bindiga aka ci zaben Jihar Kogi - Inji Lawrence Emehel

Shugaban kungiyar Justice and Peace Development Initiative wanda aka fi sani da JDPC, Lawrence Emehel, wanda ya yi aikin sa-ido a zaben Kogi ya bayyana yadda abin ya kasance.

A wata doguwar hira da Rabaren Lawrence Emehel ya yi da Jaridar Vanguard, ya bayyana bai dace a kira abin da ya faru a jihar Kogi da sunan zabe ba, domin kuwa magudi da ta’adi da aka yi.

“Na je Jihar Kogi a matsayin Mai lura da zabe, har yanzu na gaza samun yadda zan yi bayanin abin da ya faru. Abin da na gani bai yi kama da zaben da na sani inda ake fita a kada kuri’a ba.”

“Abin da na gani yaki ne. Abin da na gani ya ba ni takaici. Wannan ba zabe ba ne, tsantsar yaki kawai aka yi. Ba da yawan kuri’u aka lashe zaben ba, da karfin kan bindiga aka yi amfani.”

Sai duk da halin zaben, Darektan kungiyar ta JDPC ya bayyana cewa an samu cigaba wajen jigilar kayan aikin zaben idan aka kamanta da abin da ya faru a zaben da aka yi a farkon shekara.

KU KARANTA: Zaben Bayelsa PDP za ta kafa kwamiti domin binciken Jonathan

Lawrence Emehel ya ce kusan 40% na masu zabe ne kurum su ka fito su ka kada kuri’arsu . Malamin addinin ya ke cewa ya na tare da sauran kungiyoyin da ke kira a soke zaben jihar.

Kungiyar ta na ganin cewa da wuya kotu ra rusa zaben: “Amma kun san cewa a sha’anin korafin zabe, nasara a kotu ta danganta da abin da Alkalai su ka gani a matsayin hujja mai karfi”

Haka zalika, JDPC ta zargi Jami’an ‘yan sanda da boye shirye-shiryen da su ka yi na baza Dakaru 33, 000 da su ka yi ikirarin sun kai jihar. Emehel yace ba a ga jami’an tsaron a lokacin zabe ba.

Da aka tambayi Rabaren Emehel game da shawarar da zai bada domin a inganta zabe a kasar, sai ya bukaci a sa hannu a kudirin gyara tsarin zabe. A na sa ra’ayin zabukan 2015 sun fi na yanzu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel