Cikar dan majalisa kwana 150 a Ofis: Pantami ya ziyarci Kano, ya raba na'ura mai kwakwalwa ga dalibai 150

Cikar dan majalisa kwana 150 a Ofis: Pantami ya ziyarci Kano, ya raba na'ura mai kwakwalwa ga dalibai 150

Ministan sadarwa da sabon tattalin arziki da ya dogara da fasahar zamani, Dakta Isa Pantami, ya ziyarci jihar Kano domin murnar taya mamba mai wakiltar karamar hukumar Birnin Kano a majalisar wakilai, Sha'aban Sharada, murnar cika kwanaki 150 a ofis.

Yayin taron, wanda aka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke birnin Kano, Pantami, ya raba takardar izinin fara aiki ga wasu cibiyoyin bayar da horo a bangaren sarrafa bayanai ta hanyar fasahar zamani (ICT) tare da raba na'urori masu kwakwalwa ga daliban makarantun sakandire.

An hango gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar, da tsohon shugaban majalisar wakilai ta kasa, Ghali Umar Na'abba, a wurin taron.

Cikar dan majalisa kwana 150 a Ofis: Pantami ya ziyarci Kano, ya raba na'ura mai kwakwalwa ga dalibai 150

Pantami da Bashir Ahmad a Kano
Source: Twitter

Cikar dan majalisa kwana 150 a Ofis: Pantami ya ziyarci Kano, ya raba na'ura mai kwakwalwa ga dalibai 150

Badaru da Pantami a Kano
Source: Twitter

Cikar dan majalisa kwana 150 a Ofis: Pantami ya ziyarci Kano, ya raba na'ura mai kwakwalwa ga dalibai 150

Ghali Na'abba da Pantami a Kano
Source: Twitter

A yau jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, an bada lambar yabon ga ministan yayin bikin bada lambar yabo ta fasahar yada labarai ta kasa da aka yi a Legas. Bikin ya samu shugabancin ministan, wanda babban daraktan kamfanin sadarwar tauraron dan Adam, Dr Abimbola Alale ya wakilta.

Idan muka duba irin tsokacin da ke fitowa daga bakin mutane, wannan ba abun mamaki bane. Bayan nadashi a matsayin ministan sadarwan Najeriya, Dr Pantami ya fifita aiyukan cigaban kasa fiye da komai da ke gabansa.

Sabon ministan, ya gayyaci duk wasu bangarorin da ke karkashin kulawar ma'aikatarsa, tare da bayyana musu umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari, do tabbatar da duk cibiyoyin gwamnati sun isar da aiyukan da aka sasu ga 'yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel