Yanzu-yanzu: Wani tsohon dan majalisar wakilai kuma jigo a PDP ya koma APC

Yanzu-yanzu: Wani tsohon dan majalisar wakilai kuma jigo a PDP ya koma APC

Tsohon dan majalisar wakilai kuma jigon jam'iyyar PDP a jihar Kogi, Sunday Karimi, ya yi watsi da jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC. Karimi, wanda ya bayyana barin jam'iyyar PDP din a takardar da ya fitar yau Lahadi, yace ya yanke wannan shawarar ne saboda wasu dalilai da ya bar wa kansa sani.

Bayan watsi da jam'iyyar da yayi a yau, ya yi alkwarin mika musu katin shaidarsa na zama mamban jam'iyyar.

Duk da har yanzu bai bayyana wacce jam'iyya zai koma ba, wasu daga cikin shakikansa a siyasa da suka zanta da wakilin jaridar Daily Trust, sun tabbatar da ya tunkari jam'iyyar APC ne don samun matsuguni.

DUBA WANNAN: Pantami ya samu lambar yabo

Karimi, babban jigo ne kuma yana daga cikin wadanda suka samar da jam'iyyar PDP a shekarar 1998. Ya taba rike kujerar mataimakin jam'iyyar na jiharsa.

Amma kuma daga baya, ya koma tsohuwar jam'iyyar ACN kuma ya yi nasarar lashe zaben kujerar majalisar wakilai a 2011.

Tsohon dan majalisar daga baya ya koma jam'iyyar PDP inda ya kara lashe zabe a shekarar 2015.

Karimi, ya fito takarar majalisar dattawa a zaben 2019 amma jam'iyyar PDP ta ciresa tun a zaben fidda gwani tare da sauran 'yan takara.

Duk da ya maka jam'iyyar PDP din a kotu, daga baya Karimi ya yanke hukunci kyale jam'iyyar tare da janye kararsa, wanda kuwa daga baya yayi hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel