Interpol: Adoke ya rubutawa Malami takarda, ya nemi ya sa baki a sake shi

Interpol: Adoke ya rubutawa Malami takarda, ya nemi ya sa baki a sake shi

Tsohon Ministan shari’an Najeriya, Mohammed Adoke, ya rubutawa Magajinsa, Abubakar Malami da kuma kungiyar ‘Yan sandan Duniya, takarda domin su sa a sake shi daga dauri.

A Ranar 11 ga Watan Nuwamba, jami’an tsaro su ka damke, Mohammed Adoke a Birnin Dubai da ke kasar UAE bisa zarginsa da ake yi da hannu a wata badakalar rijiyar mai ta Malabu.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan shugaban kwamitin PACAC, Itse Sagay, ya tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya ta aika takardu zuwa birnin Dubai domin a cafke tsohon Ministan na ta.

A wata wasika da tsohon Akanta-Janar na Najeriyar ya aika zuwa Hedikwatar Interpol da ke Garin Lyon a kasar Faransa, ya bayyana cewa hukuma ba ta da wani hurumin da za ta cafke shi.

A cewarsa, an damke shi ne bisa wani umarni da tuni babban kotun tarayya ta Abuja ta yi fatali da shi. Tsohon Ministan ya bayyana wannan ne ta bakin Lauyan da ke karesa; Oluchi Uche.

KU KARANTA: Kungiya za ta sa kafar wando daya da wasu bankunan Najeriya

Lauyan ya ce:“Mun rubuto maku takarda zuwa ofishinku mai martaba ne domin sanar da ku cewa a Ranar 25 ga Watan Oktoba, Alkali DZ Senchi, ya yi fatali da umarnin cafke (M. Adoke)”

Haka zalika Lauyoyin da su ka tsayawa tsohon Ministan kasar, sun aika irin wannan wasika zuwa ga Ministan shari’an Najeriya mai-ci, Abubakar Malami, su na nema ya sa hannu a sake shi.

A wasikar da aka aiko a Ranar 14 ga Nuwamba, Lauyoyin sun nemi Mai girma Minista ya bada tabbacin cewa kotu ta yi wurgi da umarnin da aka bada na cafke shi duk inda aka same shi.

Majiyar ta ce Jami’an Interpol sun musanya cewa akwai hannunsu a cafke tsohon Ministan inda su ka daura wannan alhaki a kan gwamnatin Najeriya da kasar UAE, inda aka kama Adoke.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel