Magu: Najeriya da kasar Afrika ta Kudu su na tsara MoU kan kudin sata

Magu: Najeriya da kasar Afrika ta Kudu su na tsara MoU kan kudin sata

Mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya bayyana cewa Najeriya da Kasar Afrika ta Kudu su na tsara yarjejeniyar yadda za a dawo da dukiyar da wasu su ka sace.

Ibrahim Magu ya yi wannan jawabi ne babban birnin tarayya Abuja, a wajen taron makonni-biyu da aka shiryawa wasu jami’ai 10 na Takwarar hukumar EFCC ta kasar Liberiya watau LACC.

Yayin da Magu ya ke magana wajen rufe wannan taro da aka yi a Makarantar hukumar ta EFCC da ke Abuja, ya bayyana cewa a wannan yarjejeniya da za a kawo, za a dawo da dukiyar sata.

Abin da wannan ya ke nufi shi ne za a dawowa Najeriya kudinta da aka sace, a ka kai kasar Afrika ta Kudu. Haka zalika dukiyar Afrika ta Kudu da ta shigo Najeriya, za ta koma kasar a tsarin.

“Kun san cewa satar dukiyar al’umma laifi ne wanda bai takaita da wata kasa ba, don haka mu ka sanya hannu a MoU da kasashe da dama domin hada-kai wajen samun bayanai da rahotanni.”

KU KARANTA: Ministan Najeriya Pantami ya samu wani babban lambar yabo

Shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ya kuma bayyana cewa kasashen za su taimaka wajen aiki tare domin cafke wadanda ake zargi da laifi.

“A makon da ya gabata ina kasar Afrika ta Kudu, akwai shirin da ake yi na sa-hannu a MoU da zai bamu damar shiga kasar kai-tsaye, mu karbe dukiyar Najeriya da aka sace a ka kai kasar.”

Magu ya bayyana cewa kasar Afrika ta Kudu za ta taimaka, haka zalika Najeriya za ta yi na ta kokarin inda binciken ya zo gida. Magu ya yi wannan jawabi ne a Ranar 22 ga Watan Nuwamba.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana daga Jaridar The Cable, gwamnatin kasar Liberiya ce ta roki shugaba Buhari ya shirya irin wannan taro domin a nunawa jami’anta hanyoyin yaki da sata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel