DisCos: Ma’anar umarnin da NEC ta ba kwamiti–Fadar Shugaban kasa

DisCos: Ma’anar umarnin da NEC ta ba kwamiti–Fadar Shugaban kasa

Mun ji cewa a Ranar Juma’a, 22 ga Watan Nuwamban 2019, fadar shugaban kasa, ta yi karin-haske game da aikin da ta bada na duba yadda aka saida kamfanonin wutar lantarki a Najeriya.

Fadar shugaban kasan ta yi wannan jawabi ne domin fitar da jama’a a duhu game da aikin da majalisar NEC ta tatalin arziki ta bada, ta na mai cewa ba ta ce za a karbe kamfanonin DisCos ba.

A cewar fadar shugaban kasar, aikin da za ayi zai duba hannun jarin da jihohin Najeriya su ke da shi ne a cikin kamfanonin wutan kasar a lokacin da aka saidawa ‘yan kasuwa a shekarun baya.

“Domin fitar da mutane daga duhu da kuma warware lamarin, abin da kurum aka tattauna a taron NEC jiya shi ne duba cewa ko akwai hannun jarin jihohi a lokacin da aka saida kamfunan DisCos.”

KU KARANTA: Majalisa ta na daf da sa a hana safurar jakai a Najeriya

Hadimin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande ya ce: “A kan haka ne aka kafa kwamiti domin duba tarihin saida kamfanin tare da ba majalisar tattalin shawarar abin da ya dace.”

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zai jagoranci wannan aiki. Za a samu sauran gwamnoni daga kowane bangare na kasar nan da ke cikin kamfanin NDPHC a cikin babban kwamitin.

A 2013, gwamnatin Goodluck Jonathan ta fara shirin saidawa ‘yan kasuwa kamfanin wuta. Shekaru da-dama da gwamnati ta saida kamfanonin, har yanzu ana kukan rashin wuta a kasar.

A taron karshe na majalisar tattalin arziki wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ke jagoranta, aka kafa kwamitin da zai duba yadda aka saidawa ‘yan kasuwa kamfanonin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel