Jam’iyyar PDP za ta duba abubuwan da ke faruwa a Edo, Legas da Kano - BOT

Jam’iyyar PDP za ta duba abubuwan da ke faruwa a Edo, Legas da Kano - BOT

Majalisar amintattu watau BoT na jam’iyar PDP, ta nada wani kwamiti domin ya duba korafin da ‘ya ‘yan jam’iyyar su ke yi a jihohin da su ka hada da Edo, Kano, da Legas, da sauransu.

Shugaban majalisar amintattun jam’iyar hamayya ta PDP, Sanata Walid Jibrin, ya bayyana mana wannan a lokacin da ya ke zantawa da wasu Manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

Walid Jibrin ya ke cewa BoT ta kuma kafa kwamitoci dabam-daban domin su taimaka mata wajen ayyukan ta. Jibrin ya yi wannan jawabi ne a Ranar Juma’a, 22 ga Watan Nuwamba, 2019.

“Mun kafa kwamitoci da-dama su soma aiki musamman kwamitin sulhu da sasanta rikici, mun fahimci cewa akwai korafe-korafe masu yawa a Edo, Kano, Legas da wasu Jihohin.” Inji Jibrin.

“Bayan wannan kwamiti ya yi aikin gano gaskiyar abubuwan da su ke faruwa, za mu zauna mu duba lamarin kafin 2020.” Jibrin ya kara da cewa za su duba abin da ya faru a zabukan baya.

KU KARANTA: Ana wasan zargi tsakanin Gwamnan PDP da tsohon Gwamnan APC

Walid Jibrin ya fadawa ‘yan jarida: “BoT ta kuma nemi majalisar NWC ta kafa wani kwamiti domin binciken abin da ya faru a zaben gwamnonin da aka yi Ranar Asabar a Kogi da Bayelsa.”

Jibrin ya ce: “Mun ji zargi da martanin da ‘Ya ‘yanmu su ke yi a game da abubuwan da wasu su ka yi a musamman jihohin Kogi da Bayelsa. Za mu yi bincike kafin mu cin ma wata matsaya”

Jigon jam’iyyar adawar ya ce sun bukaci NWC ta yi tsattsauran bincike domin bin diddikin abin da ya wakana. Idan ba ku manta ba ana zargin tsohon shugaba Jonathan da yi wa APC aiki.

Shugaban na BoT ya koka da irin ta’adin da aka yi a wadannan zabuka na gwamnonin Bayelsa da Kogi, tare da kira ga jam’iyya ta duba lamarin wata jagorar PDP da aka hallaka a jihar Kogi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel