Rawar da Dino Melaye ya taka a sabon fim dinsa

Rawar da Dino Melaye ya taka a sabon fim dinsa

- Sanannen dan siyasa, Sanata Dino Melaye ya fito a sabon fim din masana'antar Nollywood

- Ya taka rawa ne a matsayin mai girma sanata a sabon fim din, in ji mashiryin shirin

- Sanatan dai na fuskantar maimaicin zabe ne a wasu sassan mazabarsa bayan zaben 16 ga watan Nuwamba

Sanannen dan siyasar nan, Sanata Dino Melaye ya fito a sabon fim din masana'antar Nollywood, wanda za a fara nunawa a wata mai zuwa.

A wasan kwaikwayon mai suna 'Lemonade', wanda furodusa Joy Idoko ya shirya, Melaye ya taka rawar sanata ne.

Wannan ba shine karo na farko da Melaye zai fara bayyana a wasan kwaikwayin masana'antar Nollywood ba. A watan da ya gabata, an gano cewa zai fito a matsayin babban dan wasa a wani wasan kwaikwayo mai dogon zango mai suna "Equity unbound".

DUBA WANNAN: Nasarar APC: Yahaya Bello babban 'dodo' ne - Oshimhole

Wasan kwaikwayon na isar da sakon maida hankali ne a kan bada hakkoki iri daya tare da adalci a Afirka, takamaimai a kasar Najeriya.

Idan zamu tuna, kwanan nan aka kwace kujerar Melaye daga majalisar dattawa. Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC zata canza zabe a wasu sassan mazabarsa, bayan sabon zaben da aka yi a ranar 16 ga watan Nuwamba.

A yayin bayanin rawar da sanatan ya taka a wasan kwaikwayon, mashiryin shirin, Idoko ya wallafa bayanin a shafinsa na Instagram.

"Zaku so ganin wannan, sanatan Najeriya Dino Melaye, da kansa ya taka rawar gani a wasan kwaikwayo mai suna Lemonade. Wani lokacin, sai ka yi amfani da idon basira kafin ka gano abinda ke gabanka." Cewar Idoko

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel