Wata babbar mota ta take jami'in KAROTA a Kano

Wata babbar mota ta take jami'in KAROTA a Kano

Hukumar kula da cunkuson ababen hawa a jihar Kano (KAROTA) ta kara yin rashin wani jami'inta da yammacin ranar Asabar sakamakon take shi da wata babbar mota (Tirela) ta yi a kusa shatale-talen gidan man fetur na NNPC da ke unguwar Hotoro.

Mutuwar jami'in na KAROTA na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar 'yan sandan jihar Kano ta sanar da cewa ta yi nasaar cafke wani direban mota da ya tsere bayan ya take wani jami'in KAROTA mai suna Ahmad Tijjani a ranar 29 ga watan Oktoba.

Direban ya buge Tijjani ne a yayin da yake kokarin kwance masa lambar mota, sannan kuma ya tsere, sai ranar Juma'a rundunar 'yan sanda ta sanar sa kama shi.

Amma sai ga shi a ranar Lahadi, jami'in hulda da jama'a na hukumar KAROTA, Nabilisi Abubakar Kofar Na'isa, ya sanar da cewa sun kara yin rashin wani jami'in da yammacin ranar Asabar.

DUBA WANNAN: Nasarar APC: Yahaya Bello babban 'dodo' ne - Oshimhole

Jawabin ya kara da cewa jama'ar da abin ya faru a kan idonsu ne suka kama direban babban motar, suka damka shi a hannun jami'an 'yan sanda yayin da yake kokarin guduwa bayan ya take jami'in na KAROTA.

"Shi jami'in da tsautsayin ya fada a kansa sunansa Abdulrahaman Sani, kuma an garzaya da shi zuwa asibiti domin ceton ransa, amma bayan an kai shi asibitin, sai likitoci suka bayar da tabbacin cewa ya mutu.

"Shugaban hukumar KAROTA, Baffa Dan'agundi, ya nuna alhinin mutuwar jami'in tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalinsa da kuma yin gargadi ga direbobi da su guji yin wasa ko zama silar rasa rayuwar jami'an KAROTA. Ya yi gargadn cewa doka ba zata kyale duk wanda aka samu da laifin aikata hakan ba," a cewar jawabin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel