Boko Haram: Gwamna Zulum ya kawo 'yan sintiri 150 daga kasar Kamaru

Boko Haram: Gwamna Zulum ya kawo 'yan sintiri 150 daga kasar Kamaru

- Gwamnan jihar Barno, Farfesa Babagana Umara ya shigo da 'yan sintiri 150 daga Kamaru don karasa Boko Haram

- Ya shigo dasu ne don su hada kai da mafarauta, 'yan sintiri da sojin Najeriya don yakar Boko Haram

- Gwamnan ya samar musu da motocin aiki hudu tare da kayan aikin da zasu bukata don aiwatar da aiyukansu

Gwamnan jihar Barno, Farfesa Babagana Umara ya shigo da ‘yan sintiri 150 daga kasar Kamaru don tattara ragowar ‘yan ta’addan Boko Haram daga jihar.

Sabbin ‘yan sintirin daga Kamaru zasu hada kai ne da mafarautan Najeriya, da kuma ‘yan sintirin da ke taiamakawa rundunar sojin Najeriya, wajen yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram da suke yi a arewacin jihar Barno.

‘Yan kasar Kamarun, ‘yan asalin kungiyar sintirin Kesh-Kesh ne na kasar. An mika musu motocin aiki hudu da sauran kayan fada , a karamin bikin da aka shirya musu a ranar Asabar a Damasak, hedkwatar karamar hukumar Mobbar, da ke yankin tafkin Chadi.

DUBA WANNAN: Dokar bayar da kariya ga jakuna ya samu karbuwa a majalisa

Taron ya samu halartar kwamishinan kananan hukumomi da masarautun gargajiya na jihar, Sugun Mai-Mele, da dan majalisar jihar mai wakiltar mazabar Mobbar, Usman Moruma da sauran jami’an gwamnatin karamar hukumar.

Gwamnan ya bayyana shirinsa na yakar ta’addanci a jihar, ta yadda ya dauki dubban mafarauta da ‘yan sintiri daga yankuna daban-daban na arewacin Najeriya.

Yana taimakawa rundunar sojin Najeriya ta hanyar hada shirye-shiryen canzawa, tare da gyaran hali ga tubabbun ‘yan Boko Haram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel