Zargin da Matawalle yake wa Yari ba shi da tushe - APC reshen Zamfara

Zargin da Matawalle yake wa Yari ba shi da tushe - APC reshen Zamfara

Jam’iyyar APC ta kwatanta zargin da gwamnan jihar, Bello Matawalle ke wa tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari da zargi mara tushe ko makama. A ranar Alhamis, Gwamna Matawalle ya ce, ziyarar da Yari ke kaiwa jihar akai-akai ce ke kawo zubda jini.

A maida martanin jam’iyyar APC, ta hanzarta cewa wannan zargin da gwamnan ke wa wanda ya gada bashi da tushe balle makama.

A wata zantawa da manema labarai da jam’iyyar APC tayi a ranar Asabar, sakataren yada labarai na jam'iyyar, Ibrahim Danmalikin Gidan Goga ya ce, Gwamna Matawalle na kokarin rufe gazawarsa da ake zargi ne ta fuskar shawo kan matsalar tsaron jihar. Don haka ne ya dau laifin kacokan ya dorawa tsohon gwamnan.

Gwamnan ya kara da cewa, barazanar gwamnan ta kama Yarin da kanshi, ba tare da jami’an tsaro ba abin dariya ne kuma kamar wasan kwaikwayo. Ya jaddada cewa, wannan kalaman basu dace da fitowa daga bakin gwamnan ba.

DUBA WANNAN: Baiwa daga Allah: Matar da ta haifa 'ya'ya biyar a lokaci daya

Kamar yadda Danmaliki yace, tsohon gwamnan ya yi amfani da duk karfinsa don ganin ya shawo kan ta’addanci a jihar. Za a gane hakan ne in aka duba makuden kudaden da ya kashe don kawo dorewar tsaro a lokacin mulkinsa.

A don haka ne, y aba gwamna Matawalle shawarar maida hankali a kan aiyukan cigaban jihar kuma ya dena bata lokacinsa wajen fada da tsohon gwamnan da mabiyansa.

Ya ce, “Tunda Matawalle ya hau kujerarsa a watanni shida da suka gabata, bai aiwatar da wani aiki ba da zai amfani jihar.”

Danmaliki ya kara da kira ga jami’an tsaron jihar da kasa su bari gwamnan ya yi amfani dasu wajen yakar abokan hamayyarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel