Amurka ta bayar da umurnin a kamo mata shugaban Air Peace, Allen Onyema

Amurka ta bayar da umurnin a kamo mata shugaban Air Peace, Allen Onyema

- Wata kotun da ke zama a yankin Goergia na kasar Amurka ta bada umarnin cafko shugaban kamfanin Air Peace

- Ana zargin shugaban kamfanin Air Peace, Allen Onyeama da laifin damfarar banki da almundahanar kudi

- Amma Onyeama ya fito ya bayyana cewa bashi da laifi, don duk wata mu'amala ta kudi da ya danganci bankuna sai ta ratsa ta babban bankin Najeriya

Watan kotun da ke yankun Georgia na kasar Amurka ta bada umarnin cafke shugaba kuma mamallakin kamfanin jiragen sama na Air Peace, Allen Onyeama.

Kamar yadda takardar da ke umarnin cafke hamshakin attajirin ta nuna, alkalin kotun, Justin Anand ya sa hannu, ta bada umarnin ofishin babban sojan kasar ta adana shi.

Wannan yarjejeniyar da ke tsakanin Najeriya da kasar Amurka, wacce ta amince da kama dan kasar Amurka ko Najeriya da ake zargi da wani ta’addanci ce zata fara amfani.

DUBA WANNAN: Baiwa daga Allah: Matar da ta haifa 'ya'ya biyar a lokaci daya

Idan zamu tuna, yau mun tashi da labarin cewa ofishin ministan shari’a na Amurka, ya fitar da takardar da ke bayyana zargin shugaban kamfanin Air Peace din da damfara.

Ana zarginsa ne da damfarar banki da almundahanar kudi. Ya tura kudi kimanin dala miliyan ashirin daga Najeriya zuwa wani asusun banki na kasar Amurka, ta wata cibiya da ke da takardun bogi, a kan siyan wasu jiragen sama.

Shugaban sashin kudi na kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa, Ejiroghene Eghagha, ana zarginsa da damfarar banki tare da sata da ta danganci cibiyar.

Onyema ya musanta wannan zargin tare da cewa bashi da laifi, saboda duk kudaden da aka tura sai sun ratsa ta babban bankin Najeriya, kuma bai taba yin wani kasuwanci wanda ba halastacce ba.

Wannan zargin ya biyo baya ne, kwanaki kadan bayan majalisar dattawan kasar ta jinjinawa mai kamfanin jiragen saman.

Onyeama ya tallafa wajen dawo da 'yan Najeriya gida daga kasar Afirka ta Kudu kyauta, bayan kisan gillar da 'yan kasar suka dinga yi wa bakin haure.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel