Kotu za ta yanke hukunci kan bayar da belin dan Maina

Kotu za ta yanke hukunci kan bayar da belin dan Maina

Shugaban Majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a ranar Alhamis ya bayyana cewa duk wata bukata daga shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kawo inganci ga Najeriya, sannan cewa za a yi aiki kansa.

Lawan ya yi magana ne lokacin da shugaban kwamitin da ke shugaban kasa shawara kan cin hanci da rashawa, Itse Sagay ya ziyarce shi a ofishinsa a ranar Alhamis.

Sagay ya yi kira ga ayi gaggawan aiwatar da kotun masu laifi na musamman da sauran dokoki makamancin haka, cewa hakan zai taimakawa yaki da rashawa da kuma tabbatar da ganin cewar anyi nasara a yaki da rashawar.

Ya kuma roki Majalisar dattawa da ta duba batun tabbatar da mukaddashin shugaban Majalisar dattawa, Ibrahim Magu.

Lawan yace babu wata bukata a gaban majalisar dattawa na tabbatar da Shugaban EFCC.

KU KARANTA KUMA: Mun cimma nasarori da dama a wajen aiki tare da wannan majalisar dokokin tarayyar - Buhari

A wani labari makamancin haka, mun ji cewa Justice Okon Abang, babban alkalin da ke jagoranci a shari'ar Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, a jiya ya ja kunne a kan cewa kotu ba zata cigaba da lamuntar 'wasan kwaikwayo' ba yayin zaman kotu.

Alkalin ya sanar da hakan ne yayin duba bukatar dage shari'ar saboda halin rashin lafiyar da Maina ke ciki. Kuma zamansa a tsare na kara tagayyara halin da yake ciki.

Maina na fuskantar shari'a ne a kan zargin laifuka 12 da suka hada da almundahanar kudi tare da boyewa don gujewa hukunci da ake masa.

Dansa Faisal na fuskantar shari'a a gaban kotun da Maina ke fuskantar tasa a kan laifuka mabanbanta har uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel