Mun cimma nasarori da dama a wajen aiki tare da wannan majalisar dokokin tarayyar - Buhari

Mun cimma nasarori da dama a wajen aiki tare da wannan majalisar dokokin tarayyar - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce sun cimma nasarori da dama a wajen aiki tare da majalisar dokokin tarayya mai ci a yanzu.

Da yake magana a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Abuja a ranar Juma’a, 22 ga watan Nuwamba, Buhari ya bayyana cewa majalisar dokokin tarayya karkashin Shugaban majalisar dattawa mai ci ta nuna jajircewa sosai kan muhimman lamura.

“Na tursasa kaina fada maku a jiya a wajen taron masu manyan jiga-jigan jam’iyya cewa akwai lokacin da na kira Shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai, sannan na fada masu cewa zama a kan kasafin kudi tsawon watanni bakwai ba siyasa ba ne, sannan cewa ba Shugaban kasa ake kuntatawa ba, koma wanene ba mai shi ake kuntatawa ba sai kasar,” in ji shi.

“Saboda wannan dalili ina fatan fadin cewa majalisar dokokin tarayya ta tara, kamar yadda kuke karantawa a takardu, sun nuna jajircewa sosai kan muhimman lamura sannan mun cimma nasarori da dama.

“Wannan dangantaka, za mu yi kokarin ganin ya cigaba, ba zai yiwu mu bude wasu abubuwa a bainar jama’a ba amma ina ba ku tabbacin cewa mun cimma nasarori sosai.”

KU KARANTA KUMA: Duk wani bukata da Buhari zai gabatar gaban majalisa, zai amfani Najeriya – Lawan

Furucin Shugaban kasar na zuwa ne kwana daya bayan Shugaban majalisar dattawa ya ce duk wani bukata da Buhari zai aikewa majalisar dokokin tarayya zai amfani kasar sosai.

A wani ganawa da Itse Sagay, Shugaban kwamitin da ke ba Shugaban kasa shawara kan cin hanci da rashawa, a ofishinsa, Lawan ya nuna cewa a shirye suke su amince da duk wani bukata da Shugaban kasar zai gabatar.

A wani labari na daban, mun ji cewa Sanata mai wakiltan Borno ta Kudu a majalisar dokokin tarayya, Muhammad Ali Ndume ya nuna adawa kan batun kara harajin kayayyaki da gwamnatin tarayya ke shirin yi, inda ya bayyana cewa hakan zai jefa talaka a cikin mummunan yanayi.

Tun dai bayan da majalisar dattawa ta yi wa kudirin kara haraji kan kayayyaki karatu na uku a ranar Alhamis, al'amarin ke ci gaba da janyo kace-nace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel