Karin harajin kaya zai jefa talaka a cikin mummunan hali - Ndume

Karin harajin kaya zai jefa talaka a cikin mummunan hali - Ndume

Sanata mai wakiltan Borno ta Kudu a majalisar dokokin tarayya, Muhammad Ali Ndume ya nuna adawa kan batun kara harajin kayayyaki da gwamnatin tarayya ke shirin yi, inda ya bayyana cewa hakan zai jefa talaka a cikin mummunan yanayi.

Tun dai bayan da majalisar dattawa ta yi wa kudirin kara haraji kan kayayyaki karatu na uku a ranar Alhamis, al'amarin ke ci gaba da janyo kace-nace.

Sanata Ndume ya kasance daya daga cikin 'yan majalisar dattawa da ke yi wa kudirin kallon ba zai yi wa talakawan Najeriya dadi ba.

A cewarsa: "Na amince da wasu haraji-haraji da aka sanya amma wannan ban ga alfanunsa ba ga talakawa kasancewar talakawa ne suka zabe mu.

"Allah na gani ba na tare da wannan karin harajin.”

Sanata Ndume ya ce hukumomin da ke da alhakin karbar haraji sun kasa tara kudin da ya kamata su tara.

Ndume ya kara da cewa kaso 85 daga cikin kudin za a tura wa kananan hukumomi da jihohi wadanda talaka ba zai ci moriyarsa su ba.

Sai dai ya ce akwai wasu hanyoyin samar da haraji ba lallai ta hanyar kara haraji kan kayayyaki ba.

To amma Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya ce "gwamnati ta yi la'akari da talaka kafin fito da harajin," in da ya ce "harajin zai fi shafar kamfanoni."

KU KARANTA KUMA: Abba Gida-Gida ya yi martani a kan hukuncin kotun daukaka kara

A wani labarin kuma, mun ji cewa Shugaban Majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a ranar Alhamis ya bayyana cewa duk wata bukata daga shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kawo inganci ga Najeriya, sannan cewa za a yi aiki kansa.

Lawan ya yi magana ne lokacin da shugaban kwamitin da ke shugaban kasa shawara kan cin hanci da rashawa, Itse Sagay ya ziyarce shi a ofishinsa a ranar Alhamis.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel