Duk wani bukata da Buhari zai gabatar gaban majalisa, zai amfani Najeriya – Lawan

Duk wani bukata da Buhari zai gabatar gaban majalisa, zai amfani Najeriya – Lawan

- Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa ya bayyana cewa duk wani bukata daga shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai kawo inganci ga Najeriya

- Lawan ya jaddada cewar za su yi aiki domin tabbatar da bukatun shugaban kasar ba tare da bata lokaci ba

- Shugaban kwamitin da ke ba shugaban kasa shawara kan cin hanci da rashawa, Itse Sagay ya yi kira ga majalisar da ta yi gaggawan aiwatar da kudirin kotun masu laifi na musamman da sauran kudurori makamancin haka

Shugaban Majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a ranar Alhamis ya bayyana cewa duk wani bukata daga shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai kawo inganci ga Najeriya, sannan cewa za a yi aiki kansa.

Lawan ya yi magana ne lokacin da shugaban kwamitin da ke ba shugaban kasa shawara kan cin hanci da rashawa, Itse Sagay ya ziyarce shi a ofishinsa a ranar Alhamis.

Sagay ya yi kira ga ayi gaggawan aiwatar da kotun masu laifi na musamman da sauran dokoki makamancin haka, cewa hakan zai taimakawa yaki da rashawa da kuma tabbatar da ganin cewar anyi nasara a yaki da rashawar.

Ya kuma roki majalisar dattawa da ta duba batun tabbatar da mukaddashin shugaban Majalisar dattawa, Ibrahim Magu.

Lawan yace babu wani bukata a gaban majalisar dattawa mai ci na tabbatar da Magu a matsayin Shugaban EFCC.

KU KARANTA KUMA: Matar wani masoyin Buhari da gwamnan PDP ya tsare ta nemi taimakon shugaban kasa

Sai dai ya jaddada cewa, majalisar dattawan a shirye take don tabbatar da Ibrahim Magu matukar shugaban kasar ya mika bukatar hakan ga majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel