Dalilin da yasa fusatattun shugabannin APC suka nema Oshiomhole ya sauka kujerarsa

Dalilin da yasa fusatattun shugabannin APC suka nema Oshiomhole ya sauka kujerarsa

Wasu fusatattun shuwagabannin jam'iyyar APC, sun yi kira ga shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, da yayi murabus daga kujerarsa domin hakan zai kare jam'iyyar daga "rushewa".

Shugaban jam'iyyar reshen jihar Zamfara, Lawal Liman, wanda ya jagoranci fusatattun shuwagabannin jam'iyyar, ya yi wannan kiran ne a ranar Juma'a inda yayi magana da manema labarai a Abuja.

Liman yace murabus din Oshiomhole zai taimakawa jam'iyyar ta daidaita, kuma hakan zai samar da hanyar sasanci da tabbatar damokaradiyya ta gaskiya a jam'iyyar a fadin kasar nan.

Ya ce Oshiomhole ya yi amfani da ikonsa na shugaban jam'iyyar wajen umarnin aikata san ransa.

"Da yawan abubuwan arzikin da jam'iyyar ta samu, ta hanyar riko da kundin tsarin mulkinta tare da rike damokaradiyya ta gaskiya na neman rushewa. Wannan kuwa ya biyo bayan yanayin mulkin kama-karya da son rai ne na Adams Oshiomhole, wanda ke amfani da kujerarsa don yin yadda ya so," Liman ya ce.

DUBA WANNAN: APC za ta garzaya kotun koli a jihar Sokoto

"Idan muka bi kiran da shugaban kasa yayi, ya bukaci duk sassan jam'iyyar na jiha, kananan hukumomi da gudumomi, dole ne su karfafa kuma a basu girman da ya dace kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya basu," in ji shi.

Liman ya zargi Oshiomhole da yin kunnen uwar shegu da shawarar shugaban kasar ta hanyar datse duk wani tsokaci da jiga-jigan jam'iyyar zasu yi. A hakan kuma taron ya tashi ba tare da an cimma wata matsaya ba. Wannan babban abun ki ne kuma ba abun so bane.

"Daga hakkin jam'iyyar da ya rataya a kanmu da kuma hakkin mabiyanmu, babu wani abu da ya rage mu yi illa mu bukaci Oshiomhole da ya yi murabus a matsayin shugabanmu na kasa baki daya," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel