Allah ya kyauta: An kori daliban wata sakandare 71 bayan sun shiga kungiyar asiri

Allah ya kyauta: An kori daliban wata sakandare 71 bayan sun shiga kungiyar asiri

- A kalla dalibai 71 na makarantar sakandiren gwamnati da ke Etoi, karamar hukumar Uyo aka dakatar

- An dakatar da daliban ne a kan zarginsu da ake da kone makarantar tare da zama mambobin kungiyar asiri

- Kwamishinan ilimin jihar, ya ce daliban shekarar karshe a cikinsu, ba zasu rubuta jarabawar WASSCE ba

A kalla dalibai 71 na makarantar sakandiren gwamnati da ke Etoi, karamar hukumar Uyo ta jihar Akwa Ibom aka dakatar.

Kamar yadda rahoton ya nuna, an dakatar da daliban ne sakamakon zarginsu da ake da kone makarantar. Rahoton ya nuna cewa, wasu daga cikin daliban makarantar wadanda ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne, sun yanke hukuncin lalata kadarorin makarantar.

An gano cewa, daliban sun rufe shugaban makarantar na wasu sa’o’I bayan da suka hari masu gadin makarantar.

Kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Nse Essien, yayin zantawa da manema labarai a kan aukuwar lamarin, ya tabbatar da dakatar da daliban.

KU KARANTA: Innalillahi: Wata mata ta bayyana yadda take dafawa mutane abincin sayarwa da jinin al'ada

“Dukkan daliban 71 zamu dakatar kuma babu ranar dawowa, saboda mugun aikin da suka yi a makarantar. Mun samu wasu sunaye daga binciken sirri. Zamuyi hakan ne don tsaftace bangaren kuma hakan ya zama darasi ga sauran” in ji shi.

Ya kara da cewa, daliban shekarar karshe da ke cikinsu ba zasu zauna jarabawar WASSCE ba don bayyana yadda gwamnati ta ke son hana rashin da’a a makarantu.

An dorawa malaman makarantar laifi saboda yadda suka bawa daliban tarbiya mara kyau, hakan ya taka rawar gani wajen wannan mugun aikin da suka yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel