Dokar bayar da kariya ga jakuna ya samu karbuwa a majalisa

Dokar bayar da kariya ga jakuna ya samu karbuwa a majalisa

Wata kudin doka ta haramta fataucin jakuna don sayar da fatarsu ya samu karbuwa a majalisar dokokin tarayya kuma ana sa ran zai isa majalisar dattawa a mako mai zuwa.

Dan majalisa Garba Datti da ya gabatar da kudirin dokar hana fataucin jakunan ya shaidawa Daily Trust cewa, "Muna fata zuwa mako mai zuwa kudirin dokar zai isa majalisar dattawa" daga nan kuma zuwa fadar shugaban kasa da zarar majalisar dattawa ta amince da shi.

Ana sa ran sauran majalisun kasashen Afirka za suyi kuyi da wannan domin kare adadin jakuna da ake da su a kasashen nahiyar.

Wannan na zuwa ne sakamakon samun raguwar adadin jakuna da ake yi a Afirka domin fataucinsu da ake yi zuwa kasar China inda ake amfani da fatarsu wurin hada wani maganin gargajiya na inganta lafiyar fata da kara karfin mazakuta mai suna 'ejiao'.

DUBA WANNAN: Lawan ya bayyana dalilin da yasa Majalisar Dattawa bata tabbatar da Magu ba

Najeriya na cikin kasashen Africa bakwai da suka hana fataucin jakuna zuwa kasashen ketare domin kare adadin jakunan da su kayi saura.

Datti ya ce, "An hana fataucin amma babu doka a hukumance a kan hanin."

"Hakan yasa muke son muyi doka domin jami'an tsaro su samu hujjar gurfanar da masu aikata laifin safarar jakunan don fatarsu a kotu."

Cibiyar Noma ta Najeriya wacce ke da alhakin tsara dokokin a fanin noma da kiwo da saka jakuna a cikin 'dabobin da suke daf da karewa' saboda a tabbatar ba su kare a bayan kasa ba inji sakataren ma'aikatan noma da raya karkara, Mohammed Umar.

Fataucin fatar dabobi yana daga cikin jerin kayayakin da aka haramta a jerin haramtattun kayayyaki da kwastam hana shigo ko fitar da su daga Najeriya.

Umar ya ce ma'aikatan nomar tana aiki tare da Majalisar Tarayya a kan kudirin dokar don ganin an hana kashe jakunnan da safarar su zuwa kasashen waje.

"Jakuna suna da daraja a Afirka ta Yamma kamar yadda Shanu ke da daraja a India," inji Umar.

"Ba domin shanu ba da India ba sun kiyaye rayyukan shanu ba da ba su kai inda suke ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel