APC za ta garzaya kotun koli a jihar Sokoto

APC za ta garzaya kotun koli a jihar Sokoto

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Sokoto ta ce za ta garzaya kotun koli domin daukaka kara a kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na jadada nasarar Gwamna Aminu Tambuwal.

A yayin zanatawa da ya yi da manema labarai jim kadan bayan yanke hukuncin, Barrista Bashir Jodi wanda ya yi magana a madadin lauyoyin jam'iyyar ya ce jam'iyyar tana da kwararran dalilai da yasa za ta daukaka kara a kan hukuncin.

A ranar Juma'a ne dai kotun daukaka kara da tabbatar da zaben Tambuwal a matsayin hallastaccen gwamnan jihar ta Sokoto.

DUBA WANNAN: Lawan ya bayyana dalilin da yasa Majalisar Dattawa bata tabbatar da Magu ba

Kungiyar alkalan kotun da ta samu jagorancin Jastis Hussein Mukhtar, ta tabbatar da nasarar Tambuwal tare da watsi da daukaka karar da jam'iyyar APC da dan takarar gwamnanta suka yi.

Jodi ya ce, "A shari'ance, yanzu aka fara kuma babu dalilin damuwa. Muna da manyan dalilai da suka sa zamu daukaka kara zuwa kotun koli. Da taimakon Allah, muna fatan da izininshi zamu samu nasara a karshe," in ji shi.

A dayan bangaren kuma, jigon jam'iyyar APC na jihar, Sanata Aliyu Wamakko, yayin zantawa da magoya bayan jam'iyyar a jihar, yace masu kare jam'iyyar zasu yi nazari a kan hukuncin sannan su bada shawarar abinda ya dace a yi nan gaba.

"A matsayinmu na musulmai, masu imani da Ubangiji, dole ne mu dinga godiya gareshi a duk abinda ya faru. A don haka ne nake kira gareku da ku kwantar da hankulanku, ku kasanace masu bin doka tare da watsi da duk wani tashin hankali," in ji shi.

Wamakko ya kara da jinjinawa jama'ar jihar a kan kwarin gwiwarsu, soyayya da goyon bayan APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel