Da dumi-dumi: Buhari, Osinbajo da Akande sun halarci taron masu ruwa da tsaki na APC

Da dumi-dumi: Buhari, Osinbajo da Akande sun halarci taron masu ruwa da tsaki na APC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo na a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Taron ya kuma samu halartan tsohon shugaban rikon kwarya na APC, Bisi Akande.

Sauran wadanda suka hallara sun hada da gwamnoni ciki harda Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.

Buhari ya isa dakin taron ne da misalin karfe 3:15 na rana.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu masu zanga-zanga sun yi kira ga tsige Adams Oshiomhole a matsayin Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa.

Masu zanga-zangan, wadanda suka mamaye hedkwatar APC a Abuja a ranar Juma’a, 22 ya watan Nuwamba, sun kasance dauke da kwalaye da rubutu kamar irin “bankwana da Oshiomhole, “bankwana da gurbataccen shugabanci” da kuma “ya zama dole Oshiomhole ya tafi”.

KU KARANTA KUMA: Abinda muka tattauna a taron jiga-jigan APC - Oshiomhole

Sai dai kuma, wasu yan daba dauke da manyan hotunan Oshiomhole sun farma masu zanga-zangan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel