Kano: Kotun daukaka kara ta ba Gwamna Ganduje gaskiya a shari’ar 2019

Kano: Kotun daukaka kara ta ba Gwamna Ganduje gaskiya a shari’ar 2019

Yanzu nan mu ke samun labari cewa kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje a zaben jihar Kano da aka yi a farkon 2019.

Daily Nigerian ta rahoto cewa kotun ta yi watsi da daukaka karar da jam’iyyar PDP mai hamayya da ‘dan takararta watau Abba Kabir Yusuf su ka yi a watan da ya wuce.

Alkalan da su ka saurari wannan kara da aka daga a karkashin Mai shari'a Tijjani Abubakar, sun tabbatar da hukuncin da kotun sauraron korafin zabe ya yi a baya.

A cewar Daily Nigerian, an yi fatali da duka korafe-korafe har 24 da Lauyoyin jam’iyyar PDP da ‘dan takararta su ka gabatar. An yi zaman ne a yau, 22 ga Nuwamba.

KU KARANTA: Kotu ta ruguza sababbin Sarakunan da Ganduje ya nada a Kano

Alkalan Kotun daukaka karar da ke Garin Kaduna sun gamsu da hukuncin da Alkali mai shari’a Halima Shamaki ta yanke a cikin tsakiyar Watan Oktoban bana.

Idan ba ku manta ba a karshen wannan zabe da ya kai zuwa wani zagaye bayan INEC ta gaza kammala zaben a karon farko, APC ta yi nasara da kuri’a 8, 982.

Hukumar INEC ta ce Injiniya Abba Yusuf na jam’iyyar PDP ya samu 1,024,713, sannan Gwamna mai-ci na APC, Dr. Abdullahi Ganduje ya tashi da kuri’u 1, 033,695.

Bayan wannan zabe da ya zo da ce-ce-ku-ce, jam’iyyar PDP ta shigar da kara a gaban kotun da ke sauraron korafin zabe amma ba ta iya gamsar da kuliya ba.

Yanzu kotun daukaka kara ta saurari shari’ar inda ta tabbatar cewa kotun baya ta yi daidai domin kuwa jam’iyyar APC ta lashe zabe kamar yadda INEC ta fada.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel