Mutumin daya zane jami’an kiyaye haddura guda 2 ya ga ta kansa a gaban Kotu

Mutumin daya zane jami’an kiyaye haddura guda 2 ya ga ta kansa a gaban Kotu

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Osun ta gurfanar da wani matashi dan shekara 31 mai suna Olasina Olanrewaju a gaban kotun majistri dake Ile-Ife jahar Osun kan tuhumarsa da lakada ma wasu jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa, FRSC, dukan tsiya.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya ta bayyana cewa dansanda mai shigar da kara, Inspekta Sunday Osanyintuyi ya shaida ma kotu wanda ake kara ya aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Nuwamba da misalin karfe 8 na safe a shataletalen Ajebamidele, Ile-ife Osun.

KU KARANTA: Yan majalisa za su yi ma dokar N-Power garambawul domin ta kunshi matasan NYSC

Dansandan ya cigaba da zayyana ma kotu yadda lamarin ya auku, inda yace wanda ake kara Olasina ya hada kai da wasu mutane biyu wanda a yanzu sun cika wandonsu da iska wajen zane jami’an hukumar FRSC su biyu ciki da bai.

Ya kara da cewa a ranar da lamarin ya auku, Taiwo Alonge da Bello Ishola suna gudanar da aikinsu ne a kan titi sanye da kayan aiki a lokacin da Olasina da aokan nasa biyu suka yi amfani da wayar kebir wajen zane su duka su biyu, suka ji musu rauni tare da kekketa musu riguna.

Daga nan sai dansandan ya karkare jawabinsa da shaida ma kotun cewa laifukan da ake tuhumar Olasina da aikatawa sun saba ma sashi na 356(3), 451 da 516(1) na kundin hukunta manyan laifuka na shekarar 2002 na jahar Osun.

Sai dai Olasina ya musanta aikata laifin, daga na sai lauyansa, Ben Adirieji ye roki alkali ya bada belinsa a bisa sharudda masu sauki, sa’annan ya tabbatar ma kotu cewa wanda yake karewa zai cigaba da gurfana gaban kotu har a kammala shari’ar.

Daga karshe Alkalin kotun, mai sharia Bose Idowu ta bada belinsa Olasina a kan kudi N100,000 tare da mutane biyu da zasu tsaya masa a kan N100,000 kowannensu, sa’annan ta dage sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Disamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel