Masu zanga-zanga sun mamaye hedkwatar APC, sun bukaci Oshiomhole ya yi murabus

Masu zanga-zanga sun mamaye hedkwatar APC, sun bukaci Oshiomhole ya yi murabus

Wasu masu zanga-zanga sun yi kira ga tsige Adams Oshiomhole a matsayin Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa.

Masu zanga-zangan, wadanda suka mamaye hedkwatar APC a Abuja a ranar Juma’a, 22 ga watan Nuwamba, sun kasance dauke da kwalaye da rubutu kamar irin “bankwana da Oshiomhole, “bankwana da gurbataccen shugabanci” da kuma “ya zama dole Oshiomhole ya tafi”.

Sai dai kuma, wasu yan daba dauke da manyan hotunan Oshiomhole sun farma masu zanga-zangan.

Zanga-zangan na faruwa ne yan sa’o’i kadan bayan gudanar da taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Ana sanya ran Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo za su kasance a taron.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta sake tabbatar da zaben Tambuwal, ta kori karar APC

A yanzu haka an zuba matakan tsaro a sakatariyar ta APC.

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya ce a daren jiya, jiga-jigan APC sun tattauna ne a kan zaben da ya gabata, kasafin kudi, shari'o'i da lamurran da suka danganci ladabtarwa.

Da aka tambayeshi a kan sakamakon taron da ya kammalu da karafe 11:30 na dare, Oshiomhole ya ce, "Kun san taron jiga-jigan jam'iyyar ne na kasa. A takaice dai, duba ne da yadda zabukan da suka gabata suka kasance, kasafin kudin jam'iyya na shekara mai zuwa, shari'o'inmu da ke kotu sai batun ladabtarwa. Mun tattauna abubuwan da yakamata mu tattauna ne a taron shuwagabannin jam'iyyar."

A kan maganar takura ta bangaren gwamnonin APC da suka ce ya hanzarta kiran taron shuwagabannin jam'iyyar, shugaban APC na kasar ya ce, " babu wata takura. An sa ranar taron shuwagabannin kusan watanni biyu da suka gabata. Muna jiran zuwan ranar ne. Za a yi ne a ranar Juma'a. Ba ku san hakan bane?," in ji Oshiomhole.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel