Malamin addinin kirista ya yanke jiki ya mutu jim kadan bayan shigarsa jam’iyyar APC

Malamin addinin kirista ya yanke jiki ya mutu jim kadan bayan shigarsa jam’iyyar APC

Wani fitaccen malamin addinin kirista kuma fitaccen dan siyasa a jahar Edo, Fasto Aimola John ya yanke jiki ya fadi jim kadan bayan ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC tare da maigidansa Osagie Ize-Iyamu.

Shi dai Ize-Iyamu wanda shine tsohon dan takarar gwamnan jahar Edo a zaben shekarar 2016 a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya sauka sheka zuwa APC ne a ranar Alhamis, tare a tawagar magoya bayansa.

KU KARANTA: Yan bindiga sun bindige basaraken gargajiya a jahar Katsina

Daga cikin magoya bayan nasa ne akwai Fasto Aimola John, wanda ya yanke jiki a gidan Fasto Ize-Iyamu dake unguwar GRA cikin garin Bini, babban birnin jahar Edo, sai dai koda aka garzaya da shi Asibiti, likitoci sun tabbatar da cewa ya mutu tun a kan hanya.

Jaridar The Nation ta ruwaito Aimola ya taba zama dan takarar mukamin shugaban karamar hukumar Owan ta gabas a jahar Edo. Shi ma tsohon sakataren karamar hukumar Owan ta gabas, Godwin Imoudu ya tabbatar da mutuwar Aimola, inda yace ya tafi Bini da nufin sauya sheka zuwa APC ne.

A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a karamar hukumar Mangu inda suka kashe shugaban kungiyar Fulani makiyaya na Miyetti Allah reshen karamar hukumar, Sa’adu Musa Julde.

Yan bindigan sun kaddamar da harin ne a daren Laraba, 20 ga watan Nuwamba, inda suka bindige Ardo Sa’adu Musa Julde, sa’annan suka tsere cikin daji ba tare da an kama ko mutum daya daga cikinsu ba.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, wanda kuma shine shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jahar Filato, Malam Muhammad Nura Abdullahi ya tabbatar da kisan Ardo Sa’adu a shafinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel