Yanzu-yanzu: Buhari ya sake nada Aliyu Aziz a matsayin shugaban NIMC

Yanzu-yanzu: Buhari ya sake nada Aliyu Aziz a matsayin shugaban NIMC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake nada Aliyu Aziz a matsayin shugaban Hukumar Kula da tsarin shedar zama dan kasa (NIMC) a karo na biyu.

Babban manajan hukumar na sashin ayyuka da watsa labarai, Abdullahi Umar ne ya sanar da hakan cikin sakon da ya aike wa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranara Juma'a a Abuja.

Mista Umar ya ce sakon sabunta wa'addin mulkin Mista Aziz na dauke ne cikin wata wasika da sakataren gwamnatin tarayya (SGF) Boss Mustapha ya aike da ita.

DUBA WANNAN: Alkali ya ja kunne a kan 'wasan kwaikwayo' da Maina ke yi a kotu

Ya ce, "Shugaban na Najeriya ta bukaci Injiniya Aliyu Aziz ya cigaba da ayyukan alheri da ya ke yi na daga hukumar ta NIMC zuwa mataki na gaba kamar yadda ya ke a tsarin gwamnatin tarayya na riko da gaskiya da amana."

"Wannan sake nadin ya yi dai-dai da dokar NIMC da bayar da damar sabunta wa'addin shugaban hukumar sau daya bayan wa'adinsa na farko ya kare."

A cewarsa, wa'addin Mista Aziz na biyu zai fara aiki ne a ranar Juma'a 22 ga watan Nuwamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel