Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta sake tabbatar da zaben Tambuwal, ta kori karar APC

Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta sake tabbatar da zaben Tambuwal, ta kori karar APC

- Kotun daukaka kara reshen jihar Sokoto ta sake tabbatar da zaben gwamnan jihar, Alhaji Aminu Tambuwal a matsayin zababben gwamna a zaben da aka gudanar a jihar

- Kotun daukaka karar ta ce karar da APC da dan takaarta suka daukaka bai da inganci don haka ta kore shi

- A ranar 16 ya watan Oktoba ne Aliyu da APC suka daukaka kara a gaban kotun, inda suke kalubalantar hukuncin da kotun zabe ta yanke a ranar 2 ya watan Oktoba 2019, da kuma koran karar Aliyu

Kotun daukaka kara reshen jihar Sokoto a ranar Juma’a, 22 ga watan Nuwamba ta sake tabbatar da zaben gwamnan jihar, Alhaji Aminu Tambuwal a matsayin zababben gwamna a zaben da aka gudanar a jihar.

Kwamitin alkalai biyar karkashin jagorancin Justis Husseini Mukhtar, ya ce kotun daukaka karar ta riki hukuncin kotun zabe wacce a baya ta kori karar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta, Hon Ahmed Aliyu Sokoto suka shigar a kan gwamnan.

Kotun daukaka karar ta ce karar da aka daukaka bai da inganci don haka ta kore shi.

Kotun ta kuma dauki lokaci wajen magance dukkanin lamuran da aka shigar a gabanta inda wanda ake kara ya yi nasara.

Alkalai uku a kwamitin sun amince da hukunci da Justis Husseini Mukhtar ya zartar.

A ranar 16 ya watan Oktoba ne Aliyu da APC suka daukaka kara a gaban kotun, inda suke kalubalantar hukuncin da kotun zabe ta yanke a ranar 2 ya watan Oktoba 2019, da kuma koran karar Aliyu.

KU KARANTA KUMA: Kudu maso gabas: Babu gwamnan PDP da zai koma APC – Umahi

Karar ya kalubalanci kaddamar da dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Gwamna Aminu Tambuwal a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da hukumar zabe mai zaman kanta ta gudanar sa ranar 9 da kuma 23 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel