Yadda fushi ya sa na kashe mahaifina mai shekaru 72 - Matashi

Yadda fushi ya sa na kashe mahaifina mai shekaru 72 - Matashi

A ranar Alhamis, hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun cafke wasu mutane 41 da ake zargi da ta’addanci daban-daban. A ciki har da wani matashi mai shekaru 32 mai suna Ibrahim Isiaka, wanda aka zargi ta halaka mahaifinsa har lahira.

Ibrahim, mazaunin yankin Alagbaka da ke Ashi, ya ce bai kashe mahaifinsa mai suna Busari Isiaka ba da gangan ba.

Ya ce, musu mai zafi ne ya sarke tsakaninsa da mahaifinsa. Tsananin fushi ne yasa ya turosa daga saman bene, ya gangaro ta matattakala har ya mutu a hakan.

A lokacin da aka bukace ya sanar da dalilin ture mahaifinsa daga bene, ya ce, “A ranar da lamarin ya faru, na je saman bene don samunsa. Ya shirya don zai fita yayin da na tureshi. Mun saba samun sabani a kan yadda ya ke shan giya ya yi mankas. Amma a ranar bai sha ba, kawai na ture shi ne shine ya gunguro.”

DUBA WANNAN: Labari mai dadi: Kudaden da Najeriya ke samu ya bunkasa da 2.18% - NBS

Ibrahim ya bayyana cewa, mahaifiyarsa ta rasu shekaru masu yawa da suka wuce.

Dan uwan Ibrahim, Taoheed, mai shekaru 41, ya sanar da manema labarai cewa shi da dan uwansa Murtala mai shekaru 36 ba sa wajen da abun ya faru. Sun samu kiran waya ne da cewa Ibrahim ya kashe mahaifinsu sakamakon dan karamin musu.

Bayan tabbatar da faruwar lamarin, mun shirya jana’izar mahaifinmu. Bayan kwanaki uku da birne shi, ‘yan sanda suka kama dukkanmu saboda ba mu kai musu rahoto ba.

Kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar Oyo, Shina Olukolu ya ce, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, haka suma ‘yan uwan nasa sun sanar da yadda suka birne mahaifinsu da gaggawa don gudun fallasuwar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel