Lawan ya bayyana dalilin da yasa Majalisar Dattawa bata tabbatar da Magu ba

Lawan ya bayyana dalilin da yasa Majalisar Dattawa bata tabbatar da Magu ba

- Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmed Lawan, ya ce ba a tabbatar da mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa bane saboda shugaba Buhari bai turo bukatar hakan ba

- Duk da Buhari ya mika wannan bukatar ga majalisar dattawa da ta gabata, Lawan ya ce yakamata a kara turo sunan Magu ga sabuwar majalisar dattawan

- Shugaban hukumar PACAC, Itse Sagay, ya goyi bayan a tabbatar da Magu a matsayin shugaban hukumar yaki da rashawa

Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, ya bayyana dalilin da yasa majalisar tarayya ta 9 bata tabbatar da Ibrahim Magu ba a matsayin shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC ba.

Lawan ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai turo wa majalisar tarayya ta taran bukatar tabbatar da Magu ba, kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

DUBA WANNAN: Naira miliyan 5 na ke karba duk wata a matsayin fansho, inji Fashanu

Shugaban majalisar dattawan ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Nuwamba, yayin da ya karba Itse Sagay, shugaban PACAC a majalisar dattawa, Abuja.

An tura bukatar tabbatar da Magu ga majalisar dattawa ta 8 karkashin shugabancin Bukola Saraki, amma basu tabbatar da shi ba saboda wasu rahotannin tsaro da suka yi amfani dasu.

Ya bayyana cewa, majalisar dattawan a shirye take don tabbatar da Ibrahim Magu matukar shugaban kasar ya mika bukatar hakan ga majalisar.

Wannan sabuwar majalisa ce, don haka akwai bukatar shugaban kasa ya turo bukatar. Babu abinda majalisar zata iya yi,” in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel