Kudu maso gabas: Babu gwamnan PDP da zai koma APC – Umahi

Kudu maso gabas: Babu gwamnan PDP da zai koma APC – Umahi

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen Kudu maso gabas ta bayyana cewa babu ko daya daga cikin Gwamnonin yankin hudu da ke tunanin barin jam’iyyar.

Jam’iyyar ta bayyana cewa jita-jitan bai da tushe sannan cewa kawai hasashen wadanda suka kullata ne.

Mataimakin Shugaban PDP na kasa, Cif Austin Umahi a jiya Alhamis, 21 ga watan Nuwamba, ya yi watsi da rahoton da aka alakanta da wani Okechukwu Isiguzoro wanda ya kasance Shugaban kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo na kasa wanda ya yi ikirarin cewa wasu gwamnonin PDP biyu da za a ambaci sunayensu ba daga yankin sun kammala shiri tsaf domin sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Umahi a wani jawabi da ya saki Enugu ya bayyana cewa hakan ya zamo aikin Isiguzoro da mukarrabansa tun bayan da aka kunyatasu daga kasancewa ainahin jiga-jigan kungiyar Ohanaeze Ndigbo kan zargin ayyukan da suka saba ka’ida wasu yan shekaru da suka gabata.

Ya kuma gargadi kungiyar da ta janye daga yada jita-jita na karya, wanda ka iya shafar martabar shugabannin Igbpo masu mutunci ciki harda gwamnonin yankin ta hanyar amfani da sunan Ohanaeze.

Ya ce gwamnonin PDP hudu a yankin sun kasance masu jajircewa a jam’iyyar sannan cewa abun dariya ne wasu makirai su alakanta kowanne daga cikinsu da sauya sheka, don kawai su yi suna a harkar siyasa.

KU KARANTA KUMA: An yanke wa mutumin da ke yiwa sanatan Gombe sojan gona hukuncin shekara 3 a gidan yari

Jigon jam’iyyar ya jaddada cewa gwamnonin PDP na aiki kai da fata tare da shugabancin jam’iyyar a yankin domin cigaba da tabbatar da cewar kudu maso gabas ta kasance karkashin kulawa PDP da kuma kwace jihar Anambra a zaben gwamna na 2021.

A cewar Umahi, PDP karkashin jagorancinsa a yankin za ta cigaba da mayar da hankali sannan cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen gina jam’iyya mai karfi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel