Labari mai dadi: Kudaden da Najeriya ke samu ya bunkasa da 2.18% - NBS

Labari mai dadi: Kudaden da Najeriya ke samu ya bunkasa da 2.18% - NBS

Alkalluman da Hukumar Kiddiga ta Najeriya (NBS) ta fitar ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya ya kara karfi da 2.28% a cikin zango na uku na shekarar 2019.

Hakan na nuna cewa an samu karin 0.17 % a kan 2.12% da aka samu a zango na biyu na shekarar ta 2019.

A cewar rahoton tattalin arziki (GDP) da hukumar ta fitar a ranar Juma'a, kasar na samar da a kalla gangan danyen man fetur miliyan 2.04 a kullum, wannan shine adadi mafi yawa da aka samu cikin shekaru uku na baya-bayan nan.

Sai dai duk da karin adadin danyen man fetur da ake samarwa a kasar, jimlan tattalin arziki na kasar na shekara yana 6.49% ne wadda bai kai 7.17% da aka samu a zango na biyu ne shekarar ba.

Rahoton ya ce bangarorin da ba na man fetur ba sun samu karin 1.85% a zango na uku na shekarar.

DUBA WANNAN: Babbar magana: Zan bayar da umurni a kama Yari muddin aka sake kai hari a Zamfara - Matawalle

A zangon na uku, bangaren man fetur ya samar da kashi 9.77 cikin 100 ga arzikin kasar yayin da fanonin da ba na fetur ba sun samar da kashi 90.23 cikin 100.

Hakazalika, kiddigan ya nuna cewa bangaren noma ya samar da kashi 29.25 cikin 100, masana'antu sun samar da 22.17 cikin 100 yayin da ayyuka suka samar da kashi 48.59 cikin 100.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel