An yanke wa mutumin da ke yiwa sanatan Gombe sojan gona hukuncin shekara 3 a gidan yari

An yanke wa mutumin da ke yiwa sanatan Gombe sojan gona hukuncin shekara 3 a gidan yari

An yankewa wani dan damfara, Ibrahim Jumare, hukuncin shekara uku a gidan gyara halayya sakamakon yiwa wani sanatan Gombe, Danjuma Goje, sojan gona.

Alkalin babban kotun jihar Gobe, Justis Abubakar Jauro, ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, 21 ga watan Nuwamba bayan ya kama Jumare da laifin yiwa Goje sojan gona wajen damfarar wani mai neman aiki.

Matsala ya fara wa mai laifin ne lokacin da wanda ya fada tarkonsa, wani Sani Muhammad, ya aika rubutacciyar kara zuwa ga ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa reshen Gombe.

Hukumar, bayan binciken lamarin, sai ta tuhumi mai laifin da yin sojan gona wanda ya kara da sashi 321 na doka sannan hukuncinsa na karkashin sashi na 324 na dokar.

Jumare ya amsa tuhuma daya da ake masa a lokacin da ya gurfana a gaban kotu sannan biyo bayan amsa aifinsa, sai alkali ya yanke masa shekara uku a gidan yari, amma ya bashi zabin biyan tarar N40,000.

Hukumar EFCC ta kama mai laifin biyo bayan karar da Muhammad ya gabatar, inda ya yi zargin cewa an bashi wani lamba da aka ce mallakar Goje ce kan ya kira domin ya samu aiki.

A cewar Muhammad, lokacin da ya kira lambar, said an damfarar ya dunga kwaikwayon muryar Goje sannan ya umurce shi da ya kira wani Ahmed, wanda aka ce mai yana aiki tare da DPR.

KU KARANTA KUMA: Tsohon gwamnan Neja ya bukaci INEC da ta soke zabukan Kogi da Bayelsa

Lokacin da kira Ahmed, sai ya bukaci ya biya wasu kudade, wanda ya biya din, sannan ya yi mai alkawarin aiki. Duk kokari da ya yi na samun takardar daukar aiki ko dawo masa da kudin da ya biya ya ci tura, hakan ya sa shi rubuta korafi zuwa ga EFCC.

Da aka kama Jumare, sai aka same shi da layukan da aka ce na Goje da Ahmed ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel