Tirkashi: Babban fasto ya mutu jim kadan da barin shi jam'iyyar PDP ya koma APC

Tirkashi: Babban fasto ya mutu jim kadan da barin shi jam'iyyar PDP ya koma APC

- Wani babban malamin addinin kirista mai suna Fasto Aimola John ya mutu

- Babban malamin addinin kiristan ya mutu ne jim kadan bayan ya bi Osagie Ize-Iyamu wanda ya canja sheka daga jam'iyyar PDP ya koma jam'iyyar APC

- Fasto Aimola dai tsohon dan takarar kujerar shugabancin karamar hukumar Owan ta gabas ce a jihar Edo

Wani babban malamin addinin kirista mai suna Fasto Aimola John, ya fadi ya mutu jim kadan bayan yabi tawagar Pa Osagie Ize-Iyamu wanda ya canja sheka daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP ya koma babbar jam'iyya mai mulki ta APC a Benin city dake jihar Edo.

Fasto Aimola, tsohon dan takarar kujerar shugabncin karamar hukumar Owan ta gabas ne dake jihar Edo. An sanar da mutuwarshi ne bayan da aka hanzarta kaishi asibiti bayan ya fadi.

Faston ya bar babbar jam’iyyar APC ne a shekarar 2015 tare da Fasto Ize-Iyamu zuwa jam’iyyar PDP. A yanzu haka sun canza sheka daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP din a jiya zuwa APC amma sai ya fadi a gidan Ize-Iyamu.

KU KARANTA: Ga irinta nan: Wata mata ta yankewa mutumin da ya kashe mata 'yar ta bayan yayi mata fyade mazakuta

Tuni dai ake ta aika sakonnin ta’aziyya a kafafen sada zumunta na zamani a kan mutuwar Aimola. Yayin sanar da mutuwarshi, an jinjinawa Aimola a matsayin jigo kuma ginshiki ga jam'iyyar.

Tsohon sakataren karamar hukumar Owan ta gabas, Godwin Imoudu, ya tabbatar da cewa, marigayi Aimola ya je garin Benin ne don komawa jam’iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel