Matar wani masoyin Buhari da gwamnan PDP ya tsare ta nemi taimakon shugaban kasa

Matar wani masoyin Buhari da gwamnan PDP ya tsare ta nemi taimakon shugaban kasa

Matar Jospeh Odok wani lauya dake caccakar gwamnan jihar Cross Rivers, Ben Ayade ta roki Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka baki cikin tuhumar da ake yi wa maigidanta na aikata ta'addanci.

Yan sanda sun kama Mista Odok ne a ranar 26 ga watan Satumba a Abuja kuma aka tafi da shi zuwa Calabar inda aka gurfanar shi a kotu kan zargin aikata ta'addanci kuma hukuncin kisa zai iya fada wa a kansa idan laifin ta tabbata.

Lauyan Mista Odok, Oliver Osang ya shaidawa Premium Times cewa, "Abinda suke kira ta'addanci a cewar 'yan sanda shine ya hadasa rikici tsakanin 'yan garinsu da wani garin." Ya kara da cewa dalilan siyasa ne yasa ake tuhumarsa da wannan laifin da bai aikata ba.

A halin yanzu ana tsare da Mista Odok a gidan gyaran hali na garin Calabar.

Ana kyautata zaton gwamnan jihar, Mista Ayade ne ya bayar da umurnin kama lauyan duba da cewa ya dade yana caccakar gwamnatin jihar Cross Rivers.

DUBA WANNAN: Alkali ya ja kunne a kan 'wasan kwaikwayo' da Maina ke yi a kotu

A cikin wani rubutu da ya wallafa a kafa sada zumunta a Facebook, Mista Odok ya kira gwamnan 'mai barkwanci'.

"Ayade kullum burunsa shine ikirarin yin manyan ayyuka. Mene zai sa kayi magana yin babban gadan flyover alhalin gwamnatinsa ta kasa kammala ko da titi kwara daya ne tun mulkinsa na farko. Wannan wasan kwaikwayon ya fara yawa."

Ana kuma tuhumar Mista Odok ta laifin zalunci a shafin intanet saboda ya alakanta shugaban ma'aikatan Gwamna Ayade da kungiyoyin asiri.

Cecelia matar lauyan da aka tsare ta ce mijinta bai aikata laifin da ake tuhumarsa da aikatawa ba.

A cikin budaddiyar wasikar da ta rubuta zuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari a watan Nuwamba ta yi tambaya cewa "Ta yaya mutum zai aikata laifin ta'addanci ba tare da bindiga ko mabiya ba?"

A cikin wasikar, ta ce ana tsangwamar mijinta ne kawai saboda shi dan jam'iyyar APC ne kuma dan gani kashe nin Shugaba Muhammadu Buhari ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel