Tsohon gwamnan Neja ya bukaci INEC da ta soke zabukan Kogi da Bayelsa

Tsohon gwamnan Neja ya bukaci INEC da ta soke zabukan Kogi da Bayelsa

- Tsohon gwamnan jihar Neja, Dr Babangida Aliyu ya yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta soke zaben gwamna da aka gudanar a jihohin Kogi da Bayelsa

- Aliyu ya kuma yi Allah wadai da kisan Shugaban matan PDP na kwamitin kamfen din Wada a jihar Kogi, Salomi Abuh wacce yan daban siyasa suka kona har lahira a gidanta

- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata kasar ta fara nazari sosai kan tsarin zabe da kuma tabbatar da abubuwan da ya kamata ayi domin tsare damokradiyya

Tsohon gwamnan jihar Neja, Dr Babangida Aliyu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta soke zaben gwamna da aka gudanar a ranar Asabar a jihohin Kogi da Bayelsa.

Aliyu ya yi wannan kira ne a wani taron manema labarai a ranar Alhamis, 21 ga watan Nuwamba a Minna, babbar birnin jihar, ta hannun Mista Bala Bitrus, hadimin labaransa.

A cewar Aliyu: “Don haka muna bukatar hukumar INEC da gwamnati mai mulki su soke zabukan domin wanzar da zaman lafiya, ci gaban damokradiyya da kuma adalci.

“Hakan ya kasance don Salomi Acheju da dukkanin wadanda suka rasa ransu a jihohin Kogi da Bayelsa a sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Asabar da ya gabata.

“Mun bukaci gwamnatin tarayya da ta kafa kwamitoci da za su binciki lamarin cikin gaggawa da tsamo wadanda suka dauki nauyin lamarin domin yin adalci ba wai kawai yin Allah wadai da kashe-kashe da halaka kayayyaki da aka yi ba.”

Ya kuma yi Allah wadai da kisan Shugaban matan PDP na kwamitin kamfen din Wada a jihar Kogi, Salomi Abuh wacce yan daban siyasa suka kona har lahira a gidanta.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata kasar ta fara nazari sosai kan tsarin zabe da kuma tabbatar da abubuwan da ya kamata ayi domin tsare damokradiyya da ainahin manufarta a dukkanin zabuka.

KU KARANTA KUMA: Yan bindigan dake fitinar jahar Zamfara abokanka ne, ka sansu – Yari ga Matawalle

Da yake martani ga lamarin, Alhami Mohammed Imam, Shugaban jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a Neja, ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa Aliyu na son yin suna ne kawai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel