Abinda muka tattauna a taron jiga-jigan APC - Oshiomhole

Abinda muka tattauna a taron jiga-jigan APC - Oshiomhole

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya ce a daren jiya, jiga-jigan APC sun tattauna ne a kan zaben da ya gabata, kasafin kudi, shari'o'i da lamurran da suka danganci ladabtarwa.

Da aka tambayeshi a kan sakamakon taron da ya kammalu da karafe 11:30 na dare, Oshiomhole ya ce, "Kun san taron jiga-jigan jam'iyyar ne na kasa. A takaice dai, duba ne da yadda zabukan da suka gabata suka kasance, kasafin kudin jam'iyya na shekara mai zuwa, shari'o'inmu da ke kotu sai batun ladabtarwa. Mun tattauna abubuwan da yakamata mu tattauna ne a taron shuwagabannin jam'iyyar."

A kan maganar takura ta bangaren gwamnonin APC da suka ce ya hanzarta kiran taron shuwagabannin jam'iyyar, shugaban APC na kasar ya ce, " babu wata takura. An sa ranar taron shuwagabannin kusan watanni biyu da suka gabata. Muna jiran zuwan ranar ne. Za a yi ne a ranar Juma'a. Ba ku san hakan bane?, in ji Oshiomhole.

DUBA WANNAN: 'Yan fashi sun kashe dan sanda yayin balle wani banki

"Kuna magana a kan zancen Salihu ne. Wannan ra'ayinsa ne. Ko kafin ya yi magana, an sa ranar wannan taron. Muna tatauna abubuwa masu muhimmanci. Kamar yadda kuka gani, shugaban kasa ya zauna a taron har karshe." cewar Oshiomhole.

Taron jiga-jigan jam'iyyar APC din ya samu halartar shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan, kakakin majalisa Femi Gbajabiamila, Asiwaju Bola Tinubu da Chife Bisi Akande.

Taron ya samu halartar gwamonin jihohin Katsina, Kebbi, Jigawa, Kaduna, Edo, Ondo, Kogi. Sanata Ken Nnamani, Chife Audu Ogbeh, Babatunde Fashola, Godswill Akpabio, Patricia Etteh, Olusegun Osoba, Sanata Kashim Shettima, Sanata Danjuma Goje, Sanata Ahmed Yarima da mataimakin gwamnan jihar Kano da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel