Naira miliyan 5 na ke karba duk wata a matsayin fansho, inji Fashanu

Naira miliyan 5 na ke karba duk wata a matsayin fansho, inji Fashanu

Tsohon dan wasan kwallon Ingila dan asalin Najeriya, John Fashanu ya bayyana cewar har yanzu yana karbar naira miliyan 5 a duk wata a matsayin fansho daga Hukumar kula da kwallon kafa a Ingila.

Tsohon dan wasan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja yayin da ya ke bayanin dalilan da yasa 'yan Najeriya da suke kasashen waje ba sa son yin watsi da kasashen ketare su dawo Najeriya.

Ya ce ya zama dole Najeriya ta samar da albashi mai tsoka da ga tsaffin 'yan kwallo. Fashanu ya nuna goyon bayansa ga 'yan wasa kamar Tammy Abraham da Fikayo Tomori da suka zabi su buga wa Ingila wasa a maimakon kasarsu ta haihuwa wato Najeriya.

DUBA WANNAN: Babbar magana: Zan bayar da umurni a kama Yari muddin aka sake kai hari a Zamfara - Matawalle

"Har yanzu ina samun fansho da wasu allawus. Ina karbar N5m duk wata a matsayi na na tsohon dan wasan kwallon Ingila kuma yanzu shekaru na sun kai 50.

"Tammy ya san dalilin da yasa ya zabi ya buga wa Ingila wasa kuma gaskiya itace an fi kulawa da 'yan wasa a Ingila kana an fi daraja su.

"Menene dalilin da yasa muka nemi ya buga wa Najeriya wasa kuma muka wahal da shi? Dole sai mun gyara. Rashin Tammy babbar asara ce ga Najeriya. Babu wanda ya tafi Landan ya yi masa bayannin alfanun da zai samu idan zai buga wa kasarsa ta haihuwa wasa.

"Kuma idan kaji labarin abinda ya faru da Kanu Nwankwo da Jay Jay Okocha, akwai wanda ya fito don ya kare shi a kan harajinsa, ko akwai wanda ya fito ya kare Kanu yayin da ya samuy matsala da otel dinsa," Fashanu ya tambaya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel