Alkali ya ja kunne a kan 'wasan kwaikwayo' da Maina ke yi a kotu

Alkali ya ja kunne a kan 'wasan kwaikwayo' da Maina ke yi a kotu

Justice Okon Abang, babban alkalin da ke jagoranci a shari'ar Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, a jiya ya ja kunne a kan cewa kotu ba zata cigaba da lamuntar 'wasan kwaikwayo' ba yayin zaman kotu.

Alkalin ya sanar da hakan ne yayin duba bukatar dage shari'ar saboda halin rashin lafiyar da Maina ke ciki. Kuma zamansa a tsare na kara tagayyara halin da yake ciki.

Maina na fuskantar shari'a ne a kan zargin laifuka 12 da suka hada da almundahanar kudi tare da boyewa don gujewa hukunci da ake masa.

Dan sa Faisal na fuskantar shari'a a gaban kotun da Maina ke fuskantar tasa a kan laifuka mabanbanta har uku.

DUBA WANNAN: 'Yan fashi sun kashe dan sanda yayin balle wani banki

Lauyan wanda ake karar, Adeola Adedipe ya sanar da kotun cewa, bincike a kan lafiyar Maina da kuma bukatar belinsa zasu iya shafar shari'ar kai tsaye.

Amma yayin da kotun ke cigaba da sauraron martanin lauyoyin dayan bangaren, jami'in tsaro da ke aiki da kotun ya tunkari kotun don sanar da alkalin yadda ake watsa wa Maina ruwa, yayin da ya ke zaune a wajen zaman da ke karshen kotun.

A wannan lokacin ne, lauyan Maina, Francis Oronsaye, ya sanar da alkalin cewa, ya na da niyyar mika bukata ga kotun da ta bar wanda yake karewa ya sha maganinsa, amma baya son a ga kamar yana son dakatar da zaman kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel