Ga irinta nan: Wata mata ta yankewa mutumin da ya kashe mata 'yar ta bayan yayi mata fyade mazakuta

Ga irinta nan: Wata mata ta yankewa mutumin da ya kashe mata 'yar ta bayan yayi mata fyade mazakuta

- Wata mata mai shekaru 23 tare da sirikarta da kawarta sun tsinke mazakutar wani mutumi

- Sun yi hakan ne don daukar fansar lalata tare da kashe ‘yarsu da yayi a watan Augusta

- Hukumar ‘yan sanda ta ce, bata kama shi bane saboda babu kwakkwarar shaidar shi ya aikata hakan

Wata mata mai shekaru 23 mai suna Veronique Makwena ta gurfana a gaban kotun majistare ta Port Elizabeth a ranar Laraba 20 ga watan Nuwamba a kan zarginta da ake da cin zarafin da tayi na tsinkewa wani mutumi mazakuta, wanda take zargi da lalatawa tare da kashe ‘yarta mai shekaru 5 a watan Augustan da ya gabata.

An gurfanar da Makwena tare da sirikarta, Noxolo Manelin da kawarsu Siyabong Pakade a kan laifin kisan kai.

An kama mutumin da ake zargin bayan da aka ga gawar yarinyar. Amma sai ‘yan sanda suka sakeshi bayan kwanaki biyu.

Mai Magana da yawun hukumar ‘yan sandan, Alwin Labansa yace, an saki mutumin ne kafin a kammala bincike. Labansa ya kara da cewa, ana jiran sakamakon gwajin DNA da aka yi.

A ranar 2 ga watan Augusta ne mahaifiyar Chantelle ta fita ta bar su tare da kawarta a gida saboda yarinyar bata da lafiya. Daga baya sai aka nemi yarinyar aka rasa. Sun nemeta amma babu amo balle labari.

KU KARANTA: Labari mai dadi: An bude jami'ar kudi ta farko a jihar Jigawa

Mahaifiyarta ta bayyana tashin hankalin da ta shiga. Sun ga takalmin yarinyar duk da kuwa ba halinta bane yawo ba takalmi. Hakan yasa suka zargi saceta aka yi.

Washegari ne suka tsinci gawarta jina-jina a wani bandaki.

A watan Satumba ne matan suka fuskanci wanda suke zargi da yin wannan aika-aikar, amma ya karyata tare da kaisu ga hukuma. An rufesu na sati biyu inda daga nan aka sakosu. Matan basu hakura ba har sai da suka tsinkewa wanda suke zargin mazakutarshi

Jami’an ‘yan sanda sun ce basu kama wanda suke zargin bane saboda babu wata gamsasshiyar shaidar da zata sa su yi hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel