Babbar magana: Zan bayar da umurni a kama Yari muddin aka sake kai hari a Zamfara - Matawalle

Babbar magana: Zan bayar da umurni a kama Yari muddin aka sake kai hari a Zamfara - Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi alkawarin kamawa tare da ladabtar da wanda ya gada, Abdulaziz Yari, matukar akwai hannunsa a tabarbarewar tsaron jihar yayin da yake mulki.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis, yayin da ya karbi kungiyar wasu tubabbun 'yan bindiga da suka ajiye manyan makamai don nuna sukar harin da aka kai kauyen Karaye na karamar hukumar Gummi ta jihar.

"Na rantse, duk lokacin da Abdulaziz Yari ya kara shigowa gari kuma aka samu tashin hankula, zan bada umarnin cafkesa. A takaice, idan da bukata, da kaina zan jagoranci jami'an tsaro zuwa kauyensu a Talata-Mafara kuma ba wasa nake ba," Matawalle ya ja kunnen ne ta bakin mai magan da yawunsa, Zailani Bappa.

DUBA WANNAN: 'Yan fashi sun kashe dan sanda yayin balle wani banki

Gwamnan ya ce, wannan ne karo na uku da aka samu rashin zaman lafiya yayin da tsohon gwamnan ya kai zuwa jihar.

"Nasarata a matsayin gwamnan jihar da kuma nasarar kawo lumana duk rubutun Allah ne. Ba zan bar tsohon gwamnan da kawayensa su lalata min kokarina ba." cewar shi.

"Daga yanzu, zan nuna iko a hannuna yake ba a hannunsa ba. Kuma zamu yi amfani dashi don cigabanmu tare da kare miliyoyin jama'ar jihar Zamfara," gwamna ya ce.

Matawalle ya ce, Yari ya fadi warwas a lokacin da yake gwamna jihar. Hakan ta sa ya kasa tsare rayuka da kadarorin mutanen jihar, kuma ya rasa damar juya wanda ya gajesa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel