Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana ganawa da jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ta kasa da daren nan a fadar shugaban kasa, Aso Villa, Abuja gabanin taron majalisar zartarwar jam'iyyar da zai gudana gobe a hedkwatan APC.
Daga cikin wadanda ke hallare a liyafar sune babban jigon APC, Bola Ahmed Tinubu; tsohon shugaban jam'iyyar, Cif Bisi Akande; tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Sani Yarima.
Hakazalika mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; shugaban jam'iyyar ta kasa, Adams Oshiomole; shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.
A gwamnoni akwai gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar; da mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna.
Hakazalika gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi; gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari; gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng