El-Rufa'i zai jagoranci kwamitin sake duba sayar da wutar lantarki da FG ta kafa

El-Rufa'i zai jagoranci kwamitin sake duba sayar da wutar lantarki da FG ta kafa

Kwamitin koli na tattalin arzikin kasa (NEC) ya yanke shawarar sake duba yadda kamfanonin da ke raba hasken wutar lantarki (Discos) ke gudanar da harkokinsu a fadin kasa.

Da yake magana da manema labarai bayan kammala taron NEC a fadar shugaban kasa, gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, ya ce an kafa wani kwamitin wucin gadi a karkashin gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, domin sake duba matsayin kamfanonin.

Ya kara da cewa kwamitin zai kunshi ma'aikatan hukumar sayar da kadarorin gwamnati da na hukumar kula da bayar da kwangila a matsayin mambobi.

Ihedioha ya kara da cewa gwamnonin da ke wakiltar sassa 6 na Najeriya a kamfanin lantarki na yankin Neja - Delta zasu kasance a cikin kwamitin.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, shine wanda ya jagoranci zaman NEC na ranar Alhamis, 21 ga watan Nuwamba, wanda aka yi a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Kafa kwamitin na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dattijai ta umarci kwamitinta na harkokin wutar lantarki da ya binciki harkokin Discos domin gano dalilin tabarbarewar samun wutar lantarki a Najeriya.

Majalisar ta bawa kwamitin wa'adin sati hudu domin ya gabatar da rahotonsa a zaurenta domin tattauna shawarwarin da kwamitin zai bayar a kan matsalolin da ya gano.

Source: Legit

Online view pixel