'Yan fashi sun kashe dan sanda yayin balle wani banki

'Yan fashi sun kashe dan sanda yayin balle wani banki

A ranar Alhamis ne ‘yan fashi da makami suka bindige jami'in dan sanda a wani hari da suka kai wa banki a karamar hukumar Oye-Ekiti a jihar Ekiti.

Wani ganau ba jiyau ba, ya sanar da jaridar The Cable cewa, ‘yan fashin da zasu kai su goma sun fara harbi ta ko ina ne daga isarsu bankin.

Hakan kuwa ya firgita ma’aikatan bankin da kwastomomi yayin da kowa ya fara neman maboya. An ruwaito cewa, maharan sun yi amfani da wani abu mai fashewa da ke da matukar karfi wajen lalata kofar shiga bankin.

Mutane da ke zama a yankin sun tsere don neman tseratar da rayukansu yayin da ‘yan fashin suka dinga harbi a iska. ‘Yan fashin sun dinga cin karensu babu babbaka ba tare da wani kalubale daga jami’an tsaro ba.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Maina ya iso kotu domin cigaba da shari'arsa

A yayin fita daga bankin ne ‘yan fashin suka bankawa wata motar ‘yan sanda wuta. Motar dai na ajiye ne a gefen titi.

Har yanzu ba a san yawan mutanen da suka kashe ba, amma rahoto ya nuna cewa, wata karamar yarinya mai shekaru 5 ta rasa ranta. Harsashi ya sameta ne yayin da take dawowa daga makaranta.

Bankuna a yankunan karkara sun dade suna fuskantar kalubalen tsaro.

A ranar 5 ga watan Afirilu, 2018, wasu ‘yan fashi sun hari bankuna biyar a yankin. Sun halaka a kalla mutane 17 har da jami’an ‘yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel