Yanzu-yanzu: INEC ta alanta ranar da za'a karasa zaben Dino Melaye da Smart Adeyemi

Yanzu-yanzu: INEC ta alanta ranar da za'a karasa zaben Dino Melaye da Smart Adeyemi

Hukumar shirya zaben kasa mai zaman kanta INEC ta sanar da ranar da za'a tsageta tsakanin Sanata Dino Melaye da Sanata Smart Adeyemi a zaben kujerar majalisar dattawa na wakiltar mazabar Kogi ta yamma.

Kwamishanonin hukumar sun zanna ranar Alhamis sun tattauna kan lamarin zaben kuma sun yanke cewa ranar Asabar, 30 ga watan Nuwamba, 2019 za'a karasa zaben.

Kwamishanan INEC kan yada labarai, Festus Okoye, ya yi bayani a jawabin sanarwan cewa: "Hukumar NEC ta zannan yau Alhamis, 21 ga Nuwamba, 2019 kuma ta zabi ranar Asabar, 30 ga Nuwamba, 2019 domin karasa zaben mazabar Kogi ta yamma."

A ranar Asabar, 16 ga wata, INEC ta tabbatar da cewa ba a samu wanda ya yi nasara a zaben kujerar Majalisar dattawan yankin Kogi ta yamma ba a zaben da ya gabata.

INEC ta bayyana cewa tazarar da ke tsakanin ‘dan takarar APC wanda ya ke kan gaba, Smart Adeyemi, da kuma Sanata mai-ci, Dino Melaye, bai kai yawan kuri’un da aka soke a Mazabar ba.

An soke zabe a akwatuna har 53 da ke cikin rumfunan zabe 20 da ke fadin yankin Yammacin jihar Kogi a zaben karshen makon jiya. Wannan ya sa aka kashe kuri’u 43, 127 inji hukumar INEC.

Smart Adeyemi ya lashe kuri’a 80, 118 ne yayin da Dino Malaye na jam’iyyar hamayya ya tashi da 59, 548. Tazarar da ke tsakanin manyan ‘yan takarar na 20, 570 bai kai 43, 127 da aka soke ba.

Malamin zaben shiyyar, Olayinde Lawal, ya bayyana cewa babu wanda ya yi nasara tukuna domin kuwa doka ba ta bada dama a bayyana wanda ya lashe zabe a irin wannan yanayi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel