Tsiyar banza: Matashi ya zuba guba a cikin abincin biki a Katsina

Tsiyar banza: Matashi ya zuba guba a cikin abincin biki a Katsina

- Wani matashi mai suna Mudasiru Tanimu ya fada komar rundunar 'yan sanda bisa zarginsa da saka guba a abin shan da aka raba a wurin biki

- Rundunar 'yan sanda ta ce wani mutum, Iliya Musa, ya mutu sakamakon shan Zoborodon mai dauke da gubar

- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa, kuma rundunar na cigaba da gudanar da bincike domin ganin ta cafke daya matashin da ya gudu

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta tabbatar da kama wani matashi, Mudasiru Tanimu, mai shekaru 18, bisa zarginsa da zuba guba a cikin abin sha da aka raba a wurin wani biki a kauyen Barhim da ke yankin karamar hukumar Batagarawa a jihar.

A cikin wani jawabi mai dauke da sa hannun kakakinta (PRO), SP Gambo Isah, da ta fitar a ranar Alhamis, rundunar 'yan sandan jihar ta ce Tanimu ya hada kai da wani matashi, Nafiu Umar, mai shekaru 18 domin saka gubar a cikin abincin 'yan bikin.

"Rundunar 'yan sanda ta kama Tanimu, wanda ke zaune a kauyen Barhim.

"Ya samu taimakon wani matashi mai suna Nafiu Umar wajen aikata laifin da ake tuhumarsa da shi," a cewar SP Isah.

DUBA WANNAN: Ganduje Vs Sanusi: Kotu ta rushe sabbin sarakunan da Ganduje ya kirkira a Kano

Kakakin ya bayyana cewa yanzu haka Nafiu ya cika wandonsa da iska bayan amun labarin an kama Tanimu.

"Sun hada wata guba ne mai bugar wa da suka zuba a cikin Zoborodo da aka raba wa 'yan biki a kauyen Barhim da ke yankin karamar Batagarawa.

"Hankalin wani mutum, Iliya Musa, mai shekaru 25, da wata matashiya mai shekaru 16 ya gushe nan take bayan sun sha Zobon da matasan suka zuba gubar a ciki.

"An garzaya da su babban asibitin Katsina, inda likitoci suka tabbatar da cewa Musa ya mutu yayin da ita kuma matashiyar suka ce bata cikin hayyacinta," a cewar Kakakin rundunar 'yan sanda, SP Isah.

A cewar rundunar 'yan sandan, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, kuma rundunar na cigaba da gudanar da bincike domin ganin ta cafke daya matashin da ya gudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel