Ganduje zai jagoranci kwamitin binciken rikicin jam'iyyar APC na jihar Edo

Ganduje zai jagoranci kwamitin binciken rikicin jam'iyyar APC na jihar Edo

- Kwamitin aiyuka na kasa na jam’iyyar APC ya nada Ganduje don jagorantar kwamitin binciken rikicin jam’iyyar na jihar Edo

- An kirkiro kwamitin ne don kawo karshen rikicin jam’iyyar APC reshen jihar Edo wanda ya yi kamari

- Sakataren yada labarai na kasa na APC ya ce wannan yunkurin samo mafita ne mai dorewa tare karko

Kwamitin aiyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar APC ya nada Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje don ya jagoranci kwamitin mutum biyar don bincike a kan rikicin jam’iyyar a jihar Edo.

Sauran ‘yan kwamitin sune: Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari; tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi; tsohon gwamnan jihar Barno kuma sanata a halin yanzu, Kashin Shettima da Ahmed Wadada, sakatare.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Maina ya iso kotu domin cigaba da shari'arsa

Ana tsammanin kwamitin zai yi taro da duk wadanda rikicin ya shafa sannan ya mika abinda ya gano ga jam’iyyar APC. A cikin makonnan ne jam’iyyar ta yanke hukuncin kafa kwamitin binciken don shawo kan matsalar da ta ke cin jam’iyyar a reshenta na jihar Edo.

A takardar da sakataren yada labarai na jam’iyyar, Malam Lanre Issa-Onilu ya fitar jiya, yace wannan yunkuri ne da jam’iyyar ta dauka don samo mafita mai dorewa game da rikicin, kuma hakan zata sa jam’iyyar ta fito da karfinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel