Martanin jihar Kano a kan sauke sabbin Sarakuna

Martanin jihar Kano a kan sauke sabbin Sarakuna

Gwamnatin jihar kano ta maida martani a kan hukuncin da kotu ta yanke a yau Alhamis. Kotun ta yanke hukuncin soke sabbin manyan masarautun da gwamnatin jihar Kano ta kirkira, kuma ta tube rawunan sabbin Sarakunan masarautun.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba, ya ce: "duk da hukuncin kotun, gwamnatin har yanzu tana kallonsu ne a matsayin manyan sarakuna kuma zata cigaba da mu'amala dasu a hakan."

Legit.ng ta ruwaito yadda kotu ta soke sabbin masarautu hudun da gwamnatin jihar Kano ta kirkira.

Sabbin masarautun dai da Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce kirkira fadar su na garuruwan Bichi, Rano, Karaye da Gaya.

Mai shari'a Jastis Usman Na'Abba, a ranar Alhamis yace an kirkiri masarautun ne ba tare da bin ka'idar da kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanada ba.

Tuni zanga-zanga ta barke a masarautun da abun ya shafa bayan jama'ar garuruwan sun ji hukuncin kotun.

DUBA WANNAN: Kano: Zanga-zanga ta barke a kan sauke sabbin sarakunan Ganduje

A takardar da Malam Garba ya fitar, ya ce: "Gwamnatin jihar Kano tana nazari a kan hukuncin kotun a kan kirkirar sabbin masarautun na jihar. Zata dau matakin da ya dace bayan ta kammala hakan,"

Takardar da kwamishinan yada labaran ya sa hannu, Malam Muhammad Garba, yace abin dana sani ne yadda kotun ta yanke hukuncin nan duk da kuwa majalisar jihar na da karfin ikon yin abinda ta yi.

Hakazalika, takardar ta kara da bayyana cewa, gwamnatin jihar ba zata tankwashe kafa ba tana kallo wannan cigaban da walwalar mutanen jihar ya tafi a haka ba.

Malam Garba ya ce, duk da hukuncin kotun, gwamnatin jihar na kallon sabbin sarakunan a karagarsu ne kuma zata cigaba da mu'amala da su a hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel